Tuesday

Home Yanzu Yanzu: PDP zata sha mamaki a zaben da za a sake a Kano - Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa dan takarar jam’iyyar Peoples’ Democratic Party (PDP), Abba Kabir Yusuf, da magoya bayansa za su sha mamaki a zaben gwamna da za a sake gudanarwa a jihar.
Abba gida gida, cp wakili bajirawo singam, cp wakili, ganduje yaci zabe, wakar abba gida gida

Ganduje yace shi bai damu da tazarar da dan takarar PDP ya bashi ba duba ga abunda ya wakana a zaben da ba a kammala ba wanda ke cike da siyan kuri’u da kuma razana masu zabe da jam’iyyar adawar tayi.

Shugaban kwamitin labarai na APC a zaben 2019, Malam Muhammad Garba a wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 12 ga watan Maris ya bayyana cewa APC da dan takarar za su ci gaba da samun nasara kamar yadda Kano za ta ci gaba da kasancewa jihar APC.

Yace yayinda Ganduje zai ci gaba da jajircewa kan gudanar da zabe na gaskiya da amana, an toshe duk wata kafa da ta basu damar yin magudi, siyan kuri’u da razana masu zabe.

KU KARANTA KUMA: Music mp3: Sabuwa Wakar Saniyo M Inuwa - Tsiya Tsiya Ta Kare (Audio)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa dan takarar kujurar gawamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba magoya bayansa tabbacin cewa shine zai yi nasara yayin sake zaben gwamna a jihar.
No comments:
Write Comments