Sunday

Home Yanzu-Yanzu :- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 5 A Borno
Dakarun gamayyar sojin MNJTF, wacce ke kula da kasashen da ke fama da hare-haren Boko Haram mai Hedikwata a birnin N’Djamena dake kasar Chadi, tare da hadin gwiwar dakarun sojin Nijeriya a Borno, sun yi nasarar hallaka wasu mayakan Boko Haram 5, sannan wasu mayakan uku suka mika wuya.
Ta'addancin boko haram

Kakakin rundunar ta MNJTF Kanal Timothy Antigha, ya ce dakarun rundunar sun hallaka mayakan na Boko Haram ne a Doron Naira da ke Borno, inda kuma uku suka mika kansu a Kamaru.

Check :- High Paying Jobs Available for You.

Kanal Antihga ya kara da cewa dakarun rundunar MNJTF sun yi nasarar kamawa tare da lalata wata mota dake yiwa mayakan na Boko Haram safarar man fetur da sauran kayayyakin da suke bukata, a tsakanin Damasak, Garunda da kuma Gazabure.

Hakazalika rundunar Sojin hadin gwiwar sun kuma kwance wasu bama-bamai uku da mayakan na Boko Haram suka binne a gefen hanya.

SAUKE TA NAN
No comments:
Write Comments