Tuesday

Home Zaben Gwamnoni : Darius Ishaku Ne Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Taraba.
Gwamna mai ci, kuma dan takara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP Darius Ishaku na Taraba ne ya lashe zaben gwamnan jihar Taraba a karo na biyu, hukumar zabe mai zaman kanta ce ta bayyana Darius din a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar din da ta gabata. Jami’in zaben jihar Taraba.

darius ishaku taraba, taraba election result, darius ishaku taraba win taraba

 Farfesa Shehu Iya na jami’ar kimiyya ta tarayya da ke Yola jihar Adamawa ne ya bayyana hakan a muhallin da hukumar take tattara sakamakon zabe na jihar Taraban, Ishakun ya samu kuri’u da suka kai 520,433 wanda ya zarce na sauran abokan takarar shi. 

Sauran abokan takarar Ishaku sun hada da Sani Abubakar na jam’iyyar APC wanda ya zo na biyu ya samu kuri’u 362,735, sai tsohuwar ministar mata Sanata Aisha Alhassan ta jam’iyyar UDP wacce ta samu kuri’u 16,289 ta na a matsayi na uku, PDP ta yi nasara a kananan hukumomi 12 na jihar, APC kuwa ta samu nasara a kananan hukumomi 4.
No comments:
Write Comments