Tuesday

Home Zan tafiyar da gwamnati na ta yadda babu wanda zai juya ni - Tambuwal
Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a jiya, Litinin, 25 ga watan Maris ya ba wa mutanen jihar tabbacin cewa, babu mai juya shi a mulkinsa na biyu.

Tambuwal wins

“Zan gudanar da gwamnatin da wani ba zai juya ni ba,” inji shi, yayinda yake zantawa da manema labarai a Sokoto.
Ya bayyana cewa ba zai taba manta nasarar da yayi da kuri’u 342 ba. “Aikin Allah ne idan aka duba abunda ya faru a lokacin zabe,” cewar shi.

Zan tafiyar da gwamnati na ta yadda babu wanda zai juya ni - Tambuwal
Ya sha alwashin yin aiki ba kakkautawa domin ya sabonta yardar da mutane suka yi da gwamnatinsa a jihar.

Ya karyata batun amsa kowani kiran waya daga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da dan takarar gwamna na jam’iyar All Progressives Congress (APC), Ahmed Aliyu, da ke cewa sun taya shi murna akan nasarar da yayi.

Ya yi kira a gare su, cewa ana bukatar goyon bayansu wajen ci gaban jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ce ta farko a tarih da ta nada kwamishinoni mata uku, sakatarorin din-dn mata takwas da kuma kansiloli mata uku-uku a dukkanin kananan hukumomi 23.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta daga sauraron karar El-Zakzaky har sai baba-ta-gani .

Ya kara da cewa gwanatinsa na kashe naira miliyan 120 duk wata domin siyan ssinadarn tsaftace ruwa.

Tambuwal yace gwmnatinsa na aki tare da majalisar Sultan, shugabannin garuruwa da kuma hukumomin tsaro wajen magance ta’addanci a jihar.
No comments:
Write Comments