Friday

Home Zargin magudi: Hukumar INEC ta maidawa kasar Amurka zazzafan martani
Hukumar nan ta Najeriya mai zaman kanta dake da alhakin gudanar da zabe a kasar ta mayar wa da kasar Amurka martani akan zarge-zargen da ta yi na cewa zaben da ya gudana ba yi sahihancin da ake tunani can-can ba.
Magudin zabe, martanin inec ga Amurka, America

Tun farko dai ofishin jakadancin kasar ta Amurka ya fito da matsayar su ne game da zaben na 2019 da ya gudana a Najeriya in da suka bayyana takaicin su akan yadda suka ce an samu karacin masu kada kuri'u da kuma cinikayyar kuri'a tsakanin 'yan siyasa.

KU KARANTA: Zaben Kano: INEC ta shirya ma zabe a kananan hukumomi 28.

Haka ma dai ofishin na jakadancin Amurka ya bayyana takaicin sa akan yadda suka ce sojojin kasar sun yi ruwa sun yi tsaki a zabukan da suka gudana a wasu jahohi.
To sai dai a nasu martanin, hukumar ta INEC ta bakin mai magana da yawun Sakatariyar hukumar, Mista Rotimi Oyekanmi ya ce zaben yana da sahihanci dai dai da irin na sa kuma musamman ma fiye da wanda aka taba gudanarwa a baya a kasar.

Mista Rotimi har ila yau ya kuma bayyana cewa ai daman su ba su ce sun gudanar da zaben da bai da matsaloli ba kamar yadda ba'a taba yin sahihin zabe dari bisa dari a ko ina cikin duniya amma dai sun san sun yi kokari.

KU DUBA WANNAN : Hotuna : Shugaba Buhari Yayin Cin Abinci Da Shuwagabannin Kasashen Duniya a Faransa. 
No comments:
Write Comments