Friday

Home A karon farko an yiwa wasu birai dashen kwakwalwar Dan-Adam
Kungiyoyin kare hakkin dabbobi na duniya sun nuna hakan da aka yi bai kamata ba saboda birai din su ma suna jin zafi
Har ya zuwa yanzu birai ba su kwace duniyar nan ba. A karon farko, masana a fannin kimiyya sun sanya kwayoyin kwakwalwar dan adam a cikin birai.
biri, dashen kai,  dashen kwakwalwa

Masu binciken na kasar China sun yi amfani da kwakwalwar biri don daukar kwayoyin hallittun MCPH1, abin da suka yi imani da shi shine yana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa kwakwalwar dan Adam.

Masanan sunce biri ya fi dacewa wurin yin gwajin basira kuma ya fi sauri fiye da biran da suke daji, sannan kuma kwakwalwarsu ta fi daukar lokaci wajen bunkasa, kamar kwakwalwar mutum. Amma kuma duk da haka, kwakwalwarsu ba ta kara girma.

An sanya wa biri kwakwalwar mutum
Birai biyar ne suka haye bayan an kammala gwajin. Amma masu bincike sun ce gwajin bai saba wa dokokin kimiyya ba saboda kwayoyin halittan birai jinsin Macaque sun bambanta sosai da na mutane.

Da yawa ba su gamsu ba. RSPCA, wata kungiyar kula da hakkin dabbobi da ke kasar Birtaniya ta ce, "Birai dabbobi ne da suke jin zafi da damuwa. Kuma su na amfani da su wajen gwaje-gwajen da suka shafi dan Adam."

KU KARANTA: Jerin mutanen da sojoji suka kashe yayin kai hari akan "yan ta'adda ; Cewar Sarakunan zamfara.

An gudanar da binciken ne don gano yadda kwakwalwar dan Adam ke kara girma da bunkasa idan aka kwatanta da birai, wadanda suke da kashi 98 na kwayoyin halittun dan Adam.

Don haka masana kimiiyya suna so su gano wadanne kwayoyin halittu ne za su kara mana hazaka.

WATCH THE VIDEO
SOURCE  : LEGIT. NG
No comments:
Write Comments