Tuesday

Home Al’ajabi: Mutum Hudu Sun Mutum Garin Gyaran Rijiya A Kogi
Mutum Hudu sun rasa ransu a garin Kabba na jihar Kogi, a daidai lokacin da suke gyaran wata rijiya, inda rijiyar ta rubza da su, mai magana da yawun rundunar ‘yan Sanda na jihar Kogi, DSP William Aya ya bayyanawa manema labarai cewa; wata mata ce ta dauki mutanen hudu don su yi mata aikin gyaran rijiyar.

Al ajabi, katuwar rijiya, labarin rijiya

Mutanen da suka ransun sune, Kayode Ayeni, Niyi Jimoh, Olusanmu Sunday da Ayo Sunday, lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na yammacin jiya Litinin a Sango dake garin Kabba.

Tuni jami’an ‘yan sanda suka tono mutanen, inda aka zakulo su aka kai gawarwakin zuwa matuwaren babban asibiti garin Kabba, mutanen suna tsakanin shekara 30-35.

KARANTA KUMA : A karon farko Shugaba Buhari ya yi magana akan zaben Kano.

‘Yan sanda sun bayyana cewa matar da ta dauko mutanen su gyara mata wannan rijiyar mai gaba 25, ta fadi warwas a lokacin da ta samu wannan labarin mai cike da alhini, inda aka garzaya da ita zuwa babban asibitin garin Kabba din.
No comments:
Write Comments