Saturday

Home An gayyaci Shugaba Buhari ya zama babban bako a wani taron kasashe 140
Muhammadu Buhari zai bar Birnin Amman da ke kasar Jordan ne gobe Lahadi 7 ga Watan Afrilun 2019. Daga nan ne ake sa ran shugaban kasar na Najeriya zai gana da manyan kasar UAE a wani zama na musamman da za ayi.
buhari in jordan

Kamar yadda labari ya zo mana dazu nan, Mai Martaba Sarkin Dubai kuma Firayim Minista na kasar UAE, Sheikh Mohammed Bin Rachid Al Maktoum, shi ne ya gayyaci shugaba Buhari zuwa taron da aka shirya a cikin kasar sa.

Za a yi wannan zama ne da manyan shugabannin Duniya game da harkar bunkasa tattalin arzikin kasashe ta hanyar shigowar hannun jari. Wannan zama da za ayi yana cikin manyan taron da aka saba gani na kasashen Duniya.

KU KARANTA: Wani Malamin Arewa ya sa baki a kan batun garkuwa da mutane

DUBA WANNAN
Top3


Buhari zai ziyarci Birnin Dubai kafin ya dawo Najeriya gobe

Shugaban kasa Buhari yana cikin manyan baki da za su yi magana wajen wannan taro na-kasa. Wannan zai ba Najeriya damar yin magana a gaban manyan kamfanoni na kasashe 140 da watakila za su yi sha’awar shigowa Najeriya.

Rahoton ya kuma nuna cewa akwai yiwuwar Shugaban kasa Buhari ya gana da Firayim Ministan na UAE domin tattaunawa a kan wasu ‘Yan Najeriya da aka kama bayan sun yi wani gagarumun fashi a cikin kasar Larabawan kwanaki.
A halin yanzu dai alkalamun tattalin arziki sun nuna cewa kudin da ke shigowa Najeriya na FDI ya ragu a gwamnatin shugaba Buhari. Wannan ya ba kasar Ghana damar tserewa Najeriya a yankin nan.

READ MORE: Buhari zai ziyarci Birnin Dubai kafin ya dawo Najeriya gobe https://hausa.legit.ng/1231866-shugaba-buhari-zai-zarce-kasar-uae-idan-gama-taro-a-jordan.html
No comments:
Write Comments