Sunday

Home Atiku ba dan Nigeria Ba ne : Apc ta bayyanawa kotu
Jam’iyyar APC ta shaida wa Kotun Sauraren Kararrakin Zaben 2019 cewa dan takarar shugabancin kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba dan Najeriya ba ne.
wazirin adamawa

APC ta ce Atiku dan kasar Kamaru ne don haka bai cancanci tsayawa takarar shugabancin Najeriya.
APC ta roki kotu ta soke takarar Atiku, kuma ta bayyana cewa dukkan kuri’un da ya samu sama na milyan 11, duk haramtattu ne, domin inji APC, bai halasta ya tsaya takara ba.
A cikin martanin da APC ta shigar a kotun da Atiku ya maka Buhari, APC da INEC kara, babban lauyan da ke jagorantar lauyoyin APC, Lateef Fagbemi, ya ce an haifi Atiku a ranar 26 Ga Nuwamba, cikin 1946, a Jada, a lokacin Jada ta na karkashin ikon kasar Kamaru, kafin Turawan mulki su hade ta da Najeriya.
Don haka ita dai APC ta na ganin cewa Atiku dan Kamaru ne kenan, ba haifaffen Najeriya ba ne.

KARANTA KUMA : Dan majalissa ya fallasa yadda PDP ke shirin karbe Majalisa daga hannun APC a 2019. 
Haka nan ma APC ta a ce Atiku ba shi da hurumin kalubalanta ko tababar ilmin sakandaren Buhari, saboda lokacin da ya kamata kotu ta saurari batun satifiket na Buhari ya wuce, kuma ba hurumin kotun sauraren kararrakin zabe ba ne ta saurarin irin wannan ba’asin.
Atiku dai ya kai kara ne a kotu, ya na kalubalantar cewa an tafka masa magudi a zaben shugaban kasa da a ka gudanar a ranar 23 Ga Fabrairu, don haka ya nemi kotu ta tilasta soke zaben ta da umartar INEC ta sake wani zabe sahihi, ingantacce.
Ya kuma yi ikirarin cewa shi ne ya samu kuri’u mafiya rinjaye, amma aka murde masa.

Idan za a iya tunawa, Nnamdi Kanu, shugaban ‘yan taratsin IPOB ne ya taba cewa Atiku dan Kamaru ne.
Amma binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar, ya tabbatar da cewa dan Najeriya ne, tunda Jada a cikin Najeriya ta ke, tun kafin Turawa su ba Najeriya ‘yanci.
Kuma doka ce ta maida Jada a cikin Najeriya.

SOURCE : PREMIUM TIMES NG
No comments:
Write Comments