Saturday

Home Buba Galadima ya bayyana irin dangantakar da ke tsakanin 'yarshi da shugaba Buhari
Buba Galadima, ya ce ya na mamakin yadda aka yi ba a bawa diyarshi babban mukami ba a majalisar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa diyar tashi ta na da dangantaka mai karfi da shugaban kasar. A wata tattauna da ya yi da manema labarai, ya ce rikicin siyasa da tashin-tashina da aka yi a lokacin zaben gwamnan jihar Kano karo na biyu, ya faru ne dalilin hana kwamishinan 'yan sanda tabuka komai a jihar.

bubagaladima sons


A cewar shi:
"Wadanda su ke cewa diyata ta na aiki da shugaba Buhari, su na yi mini ba'a ne. 'Diyata kamar diya ce a wurin shugaba Buhari, saboda a al'ada duk wanda ya yi wa mace walittaka kamar uba ne ga wannan yarinyar. 'Ya ta tana da tarihi da shugaba Buhari. Ko lokacin da ta gama karatun ta a birnin Landan, ni da Buhari muka je mata bikin yaye dalibai; lokacin da za ayi aurenta, Buhari ne ya yi mata walicci. Lokacin da ta haihu dan ta na farko sunan Buhari ta saka mishi.

DUBA KUMA
Top3


DUBA WANNAN : Da duminsa: Onnoghen ya bayyana dalilin da yasa ya yi murabus 

"Sannan kuma diyata cikakkiyar 'yar Najeriya ce, ta yi aiki da mataimakin shugaban kasa tukuru domin ganin shugaba Buhari ya hau mulki, a takaice ma ita ce wacce ta jagoranci kamfen din shi a birnin tarayya. A ga ni na idan za a biya ta da irin wahalar da ta yi, kamata ya yi a bata matsayin minista. Diyata ta na da kwalin digiri guda biyu, da kuma kwaalin digirin-digirgir guda uku. "Babu wani mutum a cikin 'yan majalisar Buhari da ya ke da irin takardun ta, hatta shi shugaban kasar. Amma kuma duk da haka an hana ta wani babban mukami."

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments