Tuesday

Home Dalilin Da Yasa Buhari Ya Kulle Ni A Kurkuku – Lamido Adamawa
Lamido Adamawa, Dakta Barkindo Aliyu Mustapha, ya bayyana dalilan da ya sa rusasshiyar gwamnatin mulkin soja ta Janar Muhammadu Buhari ta jefa shi a gidan yari bayan ta kifar da gwamnatin Marigayi Shugaba Aliyu Shehu Shagari a shekarar 1983.

Dakta Barkindo Aliyu Mustapha

Barkindo Aliyu Mustapha ya yi wannan bayanin ne lokacin da ya ke tarbar shugaban shirin Wadata Communication Limited, Zubair Abdul’Rauf Idris, da tawagarsa wadanda su ka ziyarci Lamidon a fadarsa, domin su yi mi shi bayanin taro kan yaki da cin hanci da rashawa (Anti-Corruption Town Hall Meeting) wanda su ka shirya a Yola.

Lamido Barkindo ya cigaba da cewa a lokacin tsohowar jihar Gongola ya na aiki a matsayin kwamishina, sojoji su ka kwace mulki, gabadayan ‘yan siyasar da su ke rike da mukamai a lokacin an tsare su, domin a gudanar da bincike da ya ke da alaka da cin hanci da karbar rashawa.

“Ni a lokacin an bincike ni, kuma an wanke ni, bayan haka kuma a ka sake ni,” cewar Lamido Barkindo.

Lamidon, wanda ya jaddada goyon bayansa ga yaki da cin hanci da amsar rashawa, ya yabawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari bisa alkawarin magance matsalar cin hanci da rashawa a kasar.

KU KARANTA : Ke Duniya : Yadda wani matashi ya kashe mahaifinsa ya babbaka gawarsa.  

Lamido ya cigaba da cewa wasu mutane su na tsammanin zai nisanta kanshi ga gwamnatin Shugaba Buhari, saboda abinda ya faru, “amma na samu an sake ni, babu wani abu a cikin faruwar hakan,” in ji shi.

Haka kuma Lamido Adamawan ya yaba da ayyukan kungiyar ta Wadata Communication da cewa ta na bisa turbar yaki da cin hanci da rashawa da ke samun goyon bayan cibiyar MacArthur Foundation da ke US, ya ce goyon bayan cibiyar kan yaki da cin hanci da rashawar yana daga soyayyar da kasar Amurka ke yiwa kasar Nijeriya ne.

Da ya ke jawabi tunda farko shugaban shirin Wadata Communication Abdul’Rauf Idris, ya shaidawa Lamidon taron da kungiyar zata shirya kan cin hanci da rashawa da tsaftatacciyar gwamnati a jihar, da sarakunan gargajiya, malaman addini, jami’an tsaro, ‘yan jaridu ne zasu halarci taron.

Haka kuma Idris ya yabawa mai martaba Lamido Adamawa, game da bude gidan Radiyu mai cin gajeren zango (Pulaku FM) a jihar, da cewa wata sahihiyar hanyar yaki da cin hanci da rashawa ce, ta hanyar amfani da harshen Fillanci.

Malam Idris, ya kuma shaidawa Lamidon cewa kungiyar ta bada horo ga ‘yan jaridu da masu gabatar da shirye-shirye (journalists/producers) 36, kan dan Jarida mai bincike, domin kawar da cin hanci da rashawa, da ingantacciyar gwamnati.
Ya ce shirin da gidan radiyu Pulaku FM, ke gudanarwa kan cin hanci da rashawa ya haifar da da mai ido, domin kuwa wasu jami’an ‘yan sandan dake kan hanyar Yola-Fufore-Gurin, sun rage amsar kudade a hanun jama’a.

MAJIYA : LEADERSHIP.NG
No comments:
Write Comments