Wednesday

Home 'Dan gani kashenin Kwankwasiyya ya tsira bayan kwashe kwanaki 13 a hannun DSS
Wani fitaccen dan gani kashenin darikar Kwankwasiyya, Salisu Hotoro ya samu kansu da kyar bayan kwashe akalla kwanaki goma sha uku a hannun jami’an DSS, biyo bayan kamashi da suka yi a gidansa a ranar 4 ga watan Afrilu.

salisu yahaya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lauyan Salisu, Malam Hafizu Bichi ne ya tabbatar da sakin wanda yake karewa, Malam Salisu Hotoro wanda yayi kaurin suna wajen suka tare da caccakar gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje.

KU KARANTA: Mai rabo ka samu: Hukumar kwastam ta bude sahafin daukan sabbin ma'aikata 3,200.

Koda yake rahotanni sun bayyana cewa kama Salisu da DSS tayi bashi da alaka da sukar gwamnati, asalima ana zargin jami’an DSS sun kamashi ne saboda wasu kalaman batanci daya furta akan tsohon shugaban hukumar kulada tashoshin jiragen ruwa, kuma tsohon jigon Kwankwasiyya, Aminu Dabo.

Majiyarmu ta ruwaito mabiya darikar Kwankwasiyya sun yi ma Aminu Dabo caa! ne bayan wani ikirari da yayi na cewa shi kadai yake daukan nauyin yan Kwankwasiyya, tare da basu kulawar data dace kafin ya koma APC.

A hannu guda kuma, kaakakin yakin neman zaben dan takarar gwamnan jahar Kano a inuwar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, Saminu Dawakin Tofa ya danganta kama Salisu ga kokarin gwamnatin Ganduje na danne abokan hamayya, tare da yi ma Dimukradiyya karan tsaye.

Daga karshe Dawakin Tofa yayi alwashin jam’iyyar PDP ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen caccakar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gwamna Ganduje ba bisa zaluncin da yace sun yi musu a zaben gwamnan jahar Kano.
SOURCE LEGIT. NG
No comments:
Write Comments