Sunday

Home Dan majalissa ya fallasa yadda PDP ke shirin karbe Majalisa daga hannun APC a 2019
Wani sabon Sanatan APC da ba a bayyana sunan sa ba, ya bayyana cewa ‘Yan majalisan PDP su na shirya yadda majalisa za ta sake dawowa hannun su wannan karo. Sanatan yace za ayi kokarin yin zaben ‘yan majalisun ne a asirce.
Majalissar dokokin nigeria


Wannan Sanata da ya ki bayyana kan sa, ya bayyanawa majiyar mu cewa PDP za tayi amfani da Akawun majalisa wanda zai bada damar ayi aiki da dokar da aka yi aiki da ita a zaben 2015 wanda har ya kai Bukola Saraki ya zama shugaba.

KU KARANTA:Da dumi- dumi: kungiyar MOPPAN ta sasanta Ali nuhu da Adam. A zango. 

Dokokin majalisar da aka yi amfani da su a 2015, sun bada dama ne ‘yan majalisun tarayyar su zabi shugabanni a boye ba tare da Duniya ta san kuri’ar da kowane Sanata ya kada ba. Wannan Sanata na APC ya nuna hakan bai dace ba.

Sabon-shiga majalisar ya sha alwashi cewa ba za su bari ayi zaben shugabannin bana a boye ba, inda yace kusan ko ina a Duniya, a kan yi zaben wadanda za su jagoranci ragamar majalisa ne a bayyane, ba tare da wani boye-boye ba.

‘Dan majalisar ya kara da cewa a 2015, APC ta raina PDP inda yace ba su taba tunanin cewa abin da ya faru a majalisar zai farun ba, don haka yace a wannan karo, APC ba za ta sake yin irin wancan shirmen da tayi har ta rasa majalisar ba.

SOURCE LEGIT. NG
No comments:
Write Comments