Saturday

Home Dandalin Kannywood: Dalilan da suka sa zan kai Hadiza Gabon kara kotu - Amina Amal
Amal ta bayyana hakan ne ga manema labarai a wata hira da ta yi da su a cikin makonnan, ta yi maganar ne akan bidiyon da ya ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani da ya ke nuna lokacin da Hadiza Gabon ta ke dukan ta.
Amina amal pic,  hadiza gabon pic


"Na hadu da wasu lauyoyi kuma sun amince akan za su tsaya mini don kwato mini hakkina," in ji ta.
"Addu'ar da nake ita ce Allah ya sa na samu damar dawo da darajata a idon al'umma. Da irin abinda ya faru, yanzu na san mutane da yawa suna yi mini wani irin kallo, duk da cewa duk abinda ya faru dama an gama shirya shi ne domin a bata mini suna a idon duniya. A cikin bidiyon, za ku ga yadda ta ke dukana tana ci mini zarafi, fatan da nake Allah ya taimakeni na wanke bata sunan da aka yi mini."
Yayin da take bayani game da abin da ya faru tsakaninta da Hadiza Gabon, Amal ta ce: "Abin da ya faru shi ne, na sanya wani rubutu a daya daga cikin kafafen sadarwa, ban san cewa abinda na rubuta din zai batawa Hadiza Gabon rai ba, wacce ni ina daukarta a matsayin abar koyi a gurina.

"Da farko hotone na saka wanda bai dace ba, hakan ya jawo mutane da yawa suka yi ta faman magana akan hoton, sai daga baya na dan yi rubutu akan hoton.

KU KARANTA: Duba : Jerin Jihohin Nigeria Da Akafi Fama Da Rashin Aikin Yi.    

"Ni ban san cewa rubutun na wa ya bata mata rai ba, saboda ban kira sunan kowa a cikin rubutun nawa ba. A wannan ranar ina zaune a gida sai Habu Sarki, wanda yana daya daga cikin mutanen da nake ganin mutuncinsu sosai a masana'antar mu, ya kirani ya ce yana so muyi wata magana mai muhimmanci.
"Ya ce yanzu baya gari amma idan ya dawo zai kirani. Ya na dawowa ya kirani kamar yadda muka yi dashi, ina fitowa daga gida sai naga Hadiza Gabon ta na fitowa daga mota.

"Ban san cewa ta zo tare da wasu ba a cikin Keke Napep, ta na zuwa kusa dani ta rufe ni da duka. Sai Habu Sarki ya ce mu shiga cikin gida, sai gaba daya kaina ya daure saboda ban san menene ke faruwa ba. Sai na bude gida muka shiga dukan mu, amma har lokacin ba ta dai na dukana ba. Idan kun kalli bidiyon da kyau zaku ga cewa abun ya faru a cikin gidane. Bidiyon guda biyu ne, ta dake ni sosai sannan ta kwace wayata."

KU KARANTA: Manyan likitoci Biyar sun shigo Nigeria don Duba lafiyar Zakzaky.   

Ta ce Hadiza Gabon, da direban ta da wasu mutane, sun sake dukanta kwana daya bayan wancan abun ya faru, lokacin da ta je shagonta domin ta roketa akan ta bata wayarta da ta kwace a wurinta.
Ta nuna wa manema labaran ciwon da Hadiza Gabon din ta ji mata a fuskarta, domin su tabbatar da cewa ta dake ta.
No comments:
Write Comments