Monday

Home Gubar Dalma: Yara Sama Da 150 Ke Jinya A Zamfara – MSF
Wata Kungiya mai zaman kanta da ake kira da, Médecins Sans Frontières (MSF), ta ce, akalla yara 150 ne suke fama da cutan nan ta guban dalma a Jihar Zamfara, wadanda kuma suke kan karban magani a yanzun haka.
Yari zamfara

Mataimakin shugaban kungiyar a Nijeriya, Dakta Simba Tirima, ne ya bayyana hakan ranar Lahadi, a Abuja.

A cewar Tirima, kungiyar ta MSF ce ke daukar nauyin maganin da ake yi wa yaran a sa’ilin da gwamnatin tarayya da ta Jiha suke bayar da hadin kai ga kungiyar domin tabbatar da ba a bar yaran da ke kauyakun hakanan ba sakaka ta yanda za su ci gaba da kamuwa da cutar.

Shugaban kungiyar ya ce, sai dai matsalar rashin tsaro a Jihar ya hana kungiyar iya ci gaba da gudanar da aikin bayar da maganin da cutar ta shafa.

KU KARANTA WANNAN :- Tofa! : Abubuwa 5 da ba ka taba sani a kan Gwamnan Kano Ganduje ba.

Tirima ya ce, MSF ta dakatar da shirin yin maganin ga kananan yaran da cutar ta shafa a Jihar Neja, a watan Oktoba, 2018.
Mataimakin shugaban kungiyar ya ce, yara 10 ne kacal suka saura a cikin tsarin bayar da magani na kungiyar a Jihar ta Neja, an kuma hannata su ga gwamnatin Jihar ta Neja.

Akalla yara 30 ne cutar ta gubar dalma ta halaka a Jihar ta Neja, a shekarar 2015.
No comments:
Write Comments