Tuesday

Home Jiragen ruwa 6 makare da man fetur da sauran kayayyakin amfani sun iso tashar jirgin ruwan Lagas
Rahotanni sun kawo cewa jiragen ruwa tara makare da kayayyakin amfani daban-daban na shirin sauka a tashoshin jiragen ruwan Apapa da Tin-Can Island, hukumar tashoshin ruwan Najeriya (NPA) ta bayyana hakan a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu a Lagas.
Jiragen ruwa

An tattaro cewa hudu daga cikin jiragen shida na dauke da man fetur yayinda sauran biyun ke dauke da daskararrun kifi.
Jiragen ruwa 6 makare da man fetur da sauran kayayyakin amfani sun iso tashar jirgin ruwan Lagas.

Top3


Hukumar ta NPA ta kuma bayyana cewa ana sa ran jiragen kasa 26 dauke da alkama, daskararun kifi, kwantana, mai, kayayyaki, siga da fetur za sui so tashoshin ruwan a tsakanin ranar 9 ga watan Afrilu da kuma 28 ga watan Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Hukumar Raba Hasken Lantarki za ta fara tilasta sayen mita kan naira 36,991.50.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Majalisar dattawa ta bayyana cewa kudurin da za a gabatar da bunkasa harkar noma a kasar nan zai taimaka mutuka wurin habaka tattalin arziki, sannan zai taimakawa manoma da kayan aikin irin na zamani.

A jiya Litinin ne 'yan majalisar dattawa, suka tabbatar da cewa idan kudurin bunkasa harkar noma a kasar nan ya tabbata, zai kawo cigaba sosai ga tattalin arzikin kasar nan.

A cewar Sanatocin, idan kudurin ya tabbata, zai bayar da hanyar fara noma na zamani a fadin kasar na, musamman ma wuraren da suke da kasar noma mai kyau.

SOURCE LEGIT. NG
No comments:
Write Comments