Sunday

Home Kannywood : Hotunan Adam A. Zango da sabuwar amaryar sa
Zango ya angonce da wata mai suna Safiya Umar Chalawa, wacce aka fi kira da Suffy, a ranar juma'a, 26 ga watan Afrilu, da misalin karfe 2:30 na rana.
Adam a zango da amaryarsa,  amaryar adam a zango

An daura auren ne a masallacin fadar sarkin Gwandu da ke garin Gwandu, a jihar Kebbi.

Majiyar mu ta sanar da mu cewar Zango ya yi aure sau biyar a baya, ya samu 'ya'ya shida; hudu maza, biyu mata, daga mata biyar da ya aura kafin su rabu.
Adam a zango da amaryarsa,  amaryar adam a zango

Sabuwar amaryar Zango
Adam A. Zango da sabuwar amaryar sa
Adam A. Zango da amaryar sa

DUBA WANNAN: Dandalin Kannywood: Dalilan da suka sa zan kai Hadiza Gabon kara kotu - Amina Amal

Amina ce matar Zango ta farko da ya aura a shekarar 2006. Ita ce uwar yaron sa na farko, Haidar, wanda yanzu haka ya cika shekara 12 da haihuwa. Majiyar mu ta ce ba ta san abinda ya raba auren Zango da Amina ba.

Zango ya kara auren wata matar mai suna A'isha, 'yar asalin Shika ta karamar hukumar Zaria a jihar Kaduna. Ta haifa masa 'ya'ya maza uku.
Adam a zango da amaryarsa,  amaryar adam a zango

Jarumin ya auri matar sa ta uku mai suna Maryam daga jihar Nasarawa.

Daga bisani ya auri wata jarumar fim mai suna Maryam AB Yola a Lugbe, Abuja a shekarar 2013. Sun bayyana tare a cikin wani shirin fim din Hausa mai suna 'Nas'.

DUBA WANNAN: Mutane 5 Masu HAtsari a Duniya Da Ake Nemansu Ruwa a Jallo  

A shekarar 2015, Zango ya auri Ummul Kulsum daga Ngaoundere a jamhuriyar Kamaru. An yi auren a sirrance. Ummul Kulsum ce ta fara haifa wa Zango diya mace, wacce ya sanya wa suna Murjanatu.

Safiyya ko kuma Suffy kamar yadda ake kiranta, ita ce za ta kasance matar Zango ta shida da ya aura.
Majiyar mu ta ce Zango ya saki dukkan mata biyar da ya aura a baya, sai dai har yanzu ba ta san dalilin rabuwar sa da matan da ya ke aura ba.
No comments:
Write Comments