Monday

Home Ke Duniya : Yadda wani matashi ya kashe mahaifinsa ya babbaka gawarsa
Wani matashi dan shekara 24 mai suna Abuchi Onuorah ya kashe mahaifinsa mai shekaru 65, Onyiauke Onuorah, sa’annan ya kona gawarsa kurmus a kauyen Nando dake cikin karamar hukumar Anambra ta gabas, cikin jahar Anambra.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani dangin Onuorah ya bayyana cewa Abuchi ya bi mahaifinsa har cikin daki ne inda ya kashe akan zargin shine yayi dalilin mutuwar mahaifiyarsu mai shekaru 51, Okwundu Onuorah.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu : Abba Kabir Yusuf ya ziyarci Dahiru Dahiru Bauchi (Hotuna)

“Iyalan suna zargin mahaifin yayi amfani da tsafe tsafe ne wajen daura ma matarsa wani irin cuta da aka kasa gane kansa, kawai don ta halarci sunan diyarsu data haihu, alhali shi kuma ya umarceta da kada ta kuskura ta halarci bikin sunan.

“Har ma ya gargadeta da cewa idan har ta halarci sunan, ba zata dawo da rai ba, ita kuma tayi gaban kanta, ta tafi sunan, akan hanyarta ta zuwa taron sunan ne ciwo ya kamata, inda ta rasu bayan kwanaki biyu, sai dai kafin ta mutu sai da shaida ma yayanta alwashin da mahaifinsu ya dauka akanta.

“Don haka a ranar data mutu sai guda daga cikin yayanta Abuchi ya sheka dakin mahaifinsu a guje dauke da adda, inda ya sassarashi, sa’annan ya watsa masa fetir ya banka masa wuta bal! bal!.” Inji shi.

Sai dai abinka da wanda yayi laifi, bai tsaya wata wata bay a ranta ana kare, ya gudu daga kauyen, amma shugaban kauyen, Uja Egwu ya bayyana cewa sun kai kararsa ga ofishin Yansandan dake yankin, amma kaakakin Yansandan jahar Anambra, Haruna Muhammad yace bashi da masaniya game da lamarin.

MAJIYA LEGIT. NG
No comments:
Write Comments