Sunday

Home Kuma dai : An cafke 'yar Najeriya da hodar Iblis a birnin Sin
Jaridar South China Morning ta ruwaito cewa, Matar mai shekaru 37 a duniya, ta iso birnin Sin bayan ta keto hazo daga jihar Legas ta biranen Addis Ababa da kuma Habasha.
hodar ibilis,  Iblis

Da ya ke dai Hausawa na cewa mara gaskiya ko a cikin ruwa sai ya yi gumi, ya sanya jami'an Kwastam suka zargi Matar inda kuwa suka cimma nasarar bankado wannan mummunar hoda yayin bincikar ta a ranar Alhamis.

Bayan gudanar da bincike a asibitin Queen Elizabeth da ke birnin Hong Kong, an samu daurin hodar Iblis mai nauyin giram 215 da ta sakaya cikin farjin ta, ba ya ga hodar mai nauyi giram 214 da ta hadidiye.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya Nuna Takaicinsa game da rikicin taraba da Adamawa.

Duka duka dai an samu hodar Iblis mai nauyin giram 550 tattare da wannan Mata, wanda darajar kudin ta ya kai kimanin Dalar Amurka 66,900.

A watan Maris na shekarar 2016 da ta gabata, an cafke wata Mata 'yar kasar Brazil mai shekaru 42 dauke da hodar Iblis mai nauyin giram 400 da ta makale cikin farjin ta.

SOURCE  : LEGIT.NG
No comments:
Write Comments