Monday

Home Kwana Casa'in Kashi Na 3 : AREWA24 Channel.

Sabon shirin gidan talabijin na AREWA24 CHANNEL.

Lamura suna kara daukan zafi, sakamakon gabatowar zaben Gwamna, a cikin shirin an nuna inda gwamna yaje kaddamar da sabon titi da Gwamnatinsa gabatar a jihar.....
Arewa24-Channel, kwana 90, kwana casa'in, kwana casain, kwana casa'in Arewa24, kwana 90 Arewa24
Image© Arewa24-Channel

A gefe daya an nuna wani Dr a University wanda ya dage akan bazaiyiwa wata daliba alfarma ba, bayan daya kamata tana satar amsa a wajen jarrabawa, Mahaifin dalibar yana daga cikin manyan yaran Gwamna, wanda hakan yasa akaje har gida akayi masa kurarin zaa rushe kofar gidansa, tinda shima alfarma akayi masa qka bashi filin daya gina, kuma wai yayi kari inda ya ciyo hanya, kodai yayiwa daliba alfarma ya bata sakamako mai kyau, ko kuma a rushe masa gida.....

A asibiti kuma an nuna matar Gwamna ta shirya taro ga mata masu ciki, har ta kaddamar da tsarin haihuwa kyauta, tare da bawa mata masu juna biyu kayan hidimar bukin suna kyauta,.

An kuma nuna yadda wasu yan siyasar suke yin hayar mutane idan zaa kaddamar da taro irin haka, domin matan da aka tarawa matar Gwamna, hayosu akayi tare da sanyawa su aro jira jirai......

Film din Kwana Chasa'in yana kara daukar zafi sakamakon gabatowar babban zaben Gwamna.....

Wanne bangare ne yafi burgeka a shirin wannan satinWATCH NOWDUBA WANNAN : Kwana Casa'in - Kashi Na Biyu 2 - AREWA24   

NOTE :  wannan shafi bashida alaka da gidan tv na arewa24
No comments:
Write Comments