Tuesday

Home Lokacin zafi :Shin ko Ka San Cutar Sankarau?
Allah ya kawo mu shekara ta kawo mu, a daidai lokacin da aka shiga bazara akwai barazanar bolar cutar Sankarau, a wani rahoton da hukuma mai kula da bolar cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta fitar, ya bayyana a makon da ya wuce kadai mutum kusan 48 ne suka rasa ransu sanadiyyar kamuwa da cutar ta Sankarau.

Rigakafin cutar sankarau

Rahoton ya bayyana cewa; akalla mutum 541 ne a jihohi 15 ake jin sun kamo da cutar, a tsakanin watan Oktoban 2018 zuwa watan Maris din da ya gabata, sannan an tabbatar da mutuwar akalla mutum biyar a tsakanin garuruwan Leshigbe, Wawa da ke karamar hukumar Borgu ta jihar Neja, rahoton bolar wannan annobar ya jefa mutane cikin halin zullumi.

Akwai wasu iyalan da suka shaida wa malaman lafiya cewar; kusan dukkan wadanda ake zargin cutar ce ta yi sanadiyyar mutuwar su, sun yi fama da kamewar wuya, bugun zuciya da sauri, sai molewar kai a tsakanin jarirai.

Jama’a sun kara rudewa ne lokacin da aka samu rahoton bolar cutar a garin Babana dake karamar hukumar Borgun, duk da ba a tantance cutar bace ko ba ita bace, amma alamun cutar sun fi kama da na Sankarau din, ma’aikatar lafiya ta Nijeriya tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ce suna sanya idanu a wannan yankin da ake zargin cutar ta bola.
Top3

Duk da dai gwamnatin jihar Neja ta karyata rahotannin bolar cutar, wani darekta a ma’aikatar lafiya na jihar, Dakta Idris Ibrahim ya bayyana cewa babu sahihin rahoton bolar cutar a jihar, duk da ya tabbatar da mutuwar mutum takwas a wani kauye sake karamar hukumar Borgu, amma ya bayyana cewa ba cutar Sankarau bace ta yi sanadiyyar mutuwar mutanen.

Likitoci sun ce cutar ta Sankarau tana da nau’ika da dama, amma dai akwai nau’in Sankarau da kwayoyin cuta suke haifarwa ita ta fi hatsari, sannan ta na yawan shafar mutanen da suke kusa da wadanda suka kamu da cutar, sannan alamun cutar sun hada da zazzabi mai zafi, kamewar wuya, ciwon kai, haraswa da sauransu.

DUBA WANNAN : Jiragen ruwa 6 makare da man fetur da sauran kayayyakin amfani sun iso tashar jirgin ruwan Lagas.

Alamun cutar suna bayyana a jikin mutum cikin kwanaki uku da kamowa da cutar, amma likitoci sun bayyana cewa rigakafi tana matukar taimakawa wajen hana kamowa da cutar, sannan an bukaci al’umma da zarar taga wata alama ta cuta, ayi maza a garzaya asibiti.
No comments:
Write Comments