Friday

Home Manyan likitoci Biyar sun shigo Nigeria don Duba lafiyar Zakzaky.
A iya cewa wannan shine karon farko da gwamnatin Nijeria ta yarda wasu likitocin kasar waje samun damar ganawa da shugaban yan shi'a, Ml. Ibrahim Zakzaky domin duba lafiyarsa tun bayan kamashi da hukuma tayi a shekarar 2015.
free zakzaky, ml zakzaky

Majiyar ta ruwaito cewa likitocin sun samu damar ganawa da ml. Zakzaky ne bayan samun umarni daga Alkalin wata babbar kotu dake garin Kaduna, wanda ke sauraron karar da gwamnatin jahar Kaduna ta shigar da Al-Zakzaky.

Duba da halin rashin lafiya da shugaban yan shi’an yake aciki ne yasa Alkalin yayi umarni ga hukumar tsaron sirri ta dss wadanda ke rike da Zakzaky da matarsa, dasu gaggauta gayyato masa likitocin da yake so don su duba lafiyarsa data matar sa.

Tunda a farko dai lauyan Al-Zakzaky, Femi Falana ne ya nemi wannan bukata daga Alkalin kotun, bayan ya bata bayanin cewa har yanzu Zakzaky da matarsa suna fama da matsanancin ciwo sakamakon raunuka da suka samu daga harbin bindiga da Sojoji suka yi musu a yayin da suke kokarin kamasu a shekarar ta 2015.

Haka kuwa aka yi, hukumar DSS ta bi umarnin kotu, inda ta baiwa likitocin damar ganawa da Zakzaky da matarsa a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu a inda suke tsare dasu, sai dai basu bayyana ma manema labaru wata magana game da abin dake damun Malamin ba.

KU KARANTA: Yadda ake mayar da hakora suyi haske ƙal-ƙal a cikin awa daya  

Idan za’a tuna a can kwanakin baya da dadewa an yi ta yada jita jitan Malamin ya mutu a hannun DSS, inda daga bisani hukumar DSS ta karyata batun, har ma ta bayyanshi ga manema labaru, kuma ya bayyana musu cewa yana samun kulawa, amma baya jin dadi sosai.

MAJIYA : LEGIT.NG
No comments:
Write Comments