Thursday

Home Mun san komai: Da magudin zabe ka samu nasara a Kano - Abba ya caccaki Ganduje
Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa sai da gwamnan jihar mai ci a yanzu kuma dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC ya tabka magudin zabe sannan ya samu nasarar cin zaben.
uban abba ganduje,  abba gida gida

Injiniya Yusuf, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya ce tunanin Ganduje a yanzu bai wuce ya dauki hutu domin murnar abunda ya faru a ranar 23 ga watan Maris ba, zaben da a cewarsa bai cika sahihin ba.

KARANTA WANNAN : An gwabza tsakanin leburori hausawa da matasa a kudancin Najeriya.

Ya yi kirarin cewa zaben na cike da sayen kuri'u, cin zarafin masu kad'a kuri'a, tauye 'yancin dan Adam da kuma tayar da fitintinu da dai sauransu.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa, gwamnan jihar Kano, Ganduje, ya yi tsokaci kan zaben jihar da kuma zargin jam'iyyar adawa ta PDP da hada baki da rundunar 'yan sanda domin tabka magudin zabe a ranar 9 ga watan Maris, tun kafin daga bisani hukumar INEC ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammalaba.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments