Tuesday

Home Radadin Talauci : Wani mutum ya bankawa kansa wuta...
An garzaya da Nweze zuwa asibitin koyar wa na jami'ar Alex Ekwueme da ke Abakaliki domin ceto rayuwar sa bayan ya banka wa kansa wuta a bayan ajin makarantar firamare ta St. Patrik da ke unguwar Kpirikpiri, a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Talauci, ya kona kansa

Rahotanni sun bayyana cewar Nweze ya daure kafafunsa kafin ya cinna wa kansa wuta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi, Lovett Odah, ya ce suna binciken lamarin domin tabbatar da gaskiyar cewar kashe kansa ya yi.

Ana saura kwana daya ya aikata hakan, Nweze, dan asalin garin Umuogharu a karamar hukumar Ezza ta Arewa, ya yiwa makobtansa korafin cewar ya gaji da rayuwar fatara da rashi da suka sa ko ciyar da kansa ba ya iya yi.

DUBA WANNAN: Yadda ake mayar da hakora suyi haske ƙal-ƙal a cikin awa daya  

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan; " mun gaggauta aika motar daukan masu bukatar taimakon gagga wa zuwa wurin da abin ya faru bayan mun samu kira daga wani mutum.

" Yanzu haka muna kan gudanar da bincike a kan lamarin, ba mu samu isassun bayanan da zasu tabbatar mana da cewar kashe kansa ya yi ba, ko kuma wani abu ne daban ya faru ba ."

MAJIYA : LEGIT. NG
No comments:
Write Comments