Monday

Home Shugaban Kasar Aljeriya Ya Yi Murabus Bayan Muguwar Zanga-zanga
Shugaban kasar Aljeriya, Abdulazeez Bouteflika ya yi murabus bayan muguwar zanga-zanga da ta ki ci take cinyewa a kasar, rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar ya yi murabus din ne yau Litinin, inda ya amince zai fice daga ofishin shi kafin wa’adin shi na asali ya ciki, a ranar 28 ga watan Afrilun nan da muke ciki asalin wa’adin nashi zai kare.
Algeries

Wannan ya biyo bayan nacewa da masu zanga-zangar suka yi ne, musamman a kan manyan titunan birnin Algiers, inda suke nuna rashin amincewarsu da matakin da shugaban ya dauka na kafa sabuwar majalisar mulkin kasar, inda masu zanga-zangar suka bayyana majalisar a matsayin wacce ta sabawa bukatun ‘yan kasa.

KU KARANTA : Allah da Mala'iku sun san cewa zaben fidda gwanaye na jam'iyyar APC bai gudana ba a jihar Zamfara - Marafa  

Bouteflika din wanda yake fuskantar turjiya daga al’ummar kasar tunda ya bayyana anniyarshi ta sake tsayawa takara a karo na biyar, sannan ya ayyana kanshi a matsayin ministan tsaro a gwamnatin rikon kwaryar da aka kafa a jiya Lahadi.
A biyo mu don samun cikakkun labarai….
No comments:
Write Comments