Thursday

Home Soyayya batayi rana ba : Rikicin masoya ya Aika wani saurayi har lahira.
Wani matashi dan shekara 29 dake aikin tuka kwale-kwale a jahar Bayelsa, Alabo Enai ya hallaka kansa sakamakon bakin ciki daya turnukeshi bayan samun wani dan sabani tsakaninsa da budurwarsa Blessing.
Rikicin masoya, nishadin masoya

Majiyarmu ta ruwaito matashi Alabo dan haifaffen karamar hukumar Brass a jahar Bayelsa sun samu matsala ne da budurwarsa Blessing yar kabilar Ologbobiri a karamar hukumar Ijaw ta kudu, wanda hakan ta kai ga alakarsu tana tangal-tangal.

KU KARANTA: Radadin Talauci : Wani mutum ya bankawa kansa wuta...   

Duk kokarin da matashin saurayin yayi na shawo kan budurwarsa yaci tura, wanda hakan yayi sanadiyyar kashe kansa inda yayi amfani da ragar kama kifi ya daure wuyarsa daga saman bishiya, ma'ana dai ya rataye kansa, abin mamaki kuma wannan budurwa Blessing ce ta gano gawarsa a rataye.

Wani ganau ya bayyana cewa "Cikin kankanin lokaci jama"a suka taru suna kallon gawar matashin, sun mamakin dalilin da yasa ya hallaka kansa, ga shi kuma bai bar wani sako ko wata wasika ba, badurwar ta bayyana cewa sun samu matsala da saurayin nata watakila hakan ne yasa ya aikita wannan danyen hukunci.

Ita ma budurwa tayi karin haske kamar haka “Matsalar da ta faru tsakanin mu itace na fada masa ina son zan koma garinmu a kudancin Ijaw, shi kuma ya nuna bai amince da hakan ba, amma da na fahimci ranshi ya baci sai na hakura muka cigaba da zama tare, a wannan ranar daya mutu sai da nace masa yazo mu tafi wasan Easter, amma sai yaki, yace na tafi kawai.”

MAJIYA LEGIT.NG
No comments:
Write Comments