Monday

Home Tofa! : Abubuwa 5 da ba ka taba sani a kan Gwamnan Kano Ganduje ba
Mun kawo maku wasu abubuwa na musamman daga cikin tarihin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje wanda kwanan nan ne ya samu zarcewa a kan mulki a zaben da ya kawo ce-ce-ku-ce a Najeriya. Ganduje ya doke ‘Dan takarar PDP Abba Yusuf.
Ganduje , Baban Abba ganduje

Tun fiye da shekaru 20 da su ka wuce Abdullahi Ganduje ya fara haduwa da Mai gidan sa watau Rabiu Kwankwaso wanda yanzu rikici ya kaure a tsakanin su. Ga kadan daga cikin abubuwan da su ka shafi gwamnan na jihar Kano mai mulki a APC.

1. Shekaru
Mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yana cikin gwamnonin da su ka zarce kowa shekaru a Najeriya. A shekarar nan ne Gwamnan na jihar Kano zai cika shekaru 70 da haihuwa a Duniya.

2. Karatu
A bangaren karatu, za kuma a samu Gwamna Abdullahi Ganduje a gaba. Ganduje yayi karatun boko da addinin musulunci a Kano. A 1973 ne ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya inda ya samu Digirin farko.

KU KARANTA: Jerin sunayen gwamnonin da EFCC za ta tuhuma kan rashawa da zaran mulkinsu ya kare - .

Ganduje ya mallaki Digiri 4 a bangaren karatun Boko

Bayan yayi Digiri a bangaren koyar da kimiyya, Ganduje ya koma yayi Digirin Masters a Jami’ar Bayero ta Kano a harkar malanta. Ganduje ya sake komawa Zariya domin samun Digir-gir na MPA.
Bayan shekaru 8 ne Gwamna Abdullahi Ganduje ya samu shaidar Digir-digir na Daktan Boko watau PhD a Jami’ar Ibadan a 1993. Ganduje yayi karatu har ya kware ne a harkar sha’ani da tsarin shugabanci.

3. Lambar yabo
Ganduje yana cikin wadanda tsohon shugaban kasa watau Goodluck Jonathan ya ba tambarin girma na OFR a cikin shekarar 2012. Haka kuma Jami'ar Bayero ta taba karrama gwamnan a kwanaki.

4.  Siyasa
Abdullahi Ganduje mai shekaru 69 yana cikin wadanda su ka dade a siyasa. Ganduje ya kasance cikin Jagororin jam’iyyar NPN a jihar Kano tun a 1979. Ganduje yayi takarar majalisar tarayya a lokacin amma ya sha kasa.


KU KARANTA: Wata sabuwa inji yan caca: An baiwa dalibai lasisin shan sigari don fahimtar darasi - 

5. Aiki da Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso ya dauko Abdullahi Ganduje a matsayin mataimakin sa bayan ya fadi zaben fitar da gwanin da su ka gwabza tare a 1999. Bayan nan kuma Kwankwaso ya nada Ganduje a matsayin Kwamishinan harkar kananan hukumomi.
Bayan PDP ta sha kasa a zaben 2003, Kwankwaso ya dauki Abdullahi Ganduje a matsayin mai ba sa shawara a kujerar Minista. A 2011 ne Kwankwaso ya kara jawo Ganduje duk da sun sake yin takara tare, har ta kai ya mika masa ragamar mulki a 2015.
No comments:
Write Comments