Saturday

Home Wata sabuwa: Kotu ta samu sabbin hujoji a kan tuhumar almundahar N1.35bn da ake yiwa Sule Lamido.

Kotun Tarayya da ke zamanta a Maitama Abuja, a ranar Juma'a 5 ga watan Afrilu ta samu karin takardu daga Hukumar Yaki da Masu Yiwa Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC a matsayin hujoji a kan tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da wasu da ake tuhuma. Ana dai tuhumar Lamido ne tare da yaransu biyu Aminu Sule Lamido da Mustapha Sule Lamido kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Sauran da ake tuhumar tare da shi sun hada da wani Aminu Wada Abubakar da wasu kamfanoni biyu; Bamaina Holdings Limited da Speeds International Limited.
sule lamido songs

Idan ba a manta ba dai Hukumar EFCC tana tuhumar su ne da laifin damfarar jihar Jigawa zunzurutun kudi Naira Bilyan 1.35. Takardun da aka gabatarwa kotu sun hada da umurnin kotu na tilasta wakilin Bankin UBA, Longi Tupkop ya gabatar da shaidan bude asusun ajiya na kamfanin gine-gine na Dantata and Sowoe, sunayen wadanda ke da hannun jari a kamfanin da wasu bayanai na kamfanin.

DUBA KUMA
Top3


Shaidan da Tupkop ya bayar da kotu ya nuna hada-hadar kudin da akayi daga ranar 23 zuwa 26 na watan Afrilun 2013 ciki har da kudi N35,627,061.85.

KARANTA WANNAN : Hatsarin Mota: Masu Zuwa Shan Maganin Bindiga Zamfara 19 Sun Mutu A Hanya.
Mai bayar da shaidan ya ce: "A ranar 3 ga watan Afrilun 2013 an gabatar da cheque kuma an fitar da kudi amma an dawo da cheque din kuma an mayar da kudadin cikin asusun ajiyar saboda ba a tabbatar da izinin fitar da kudaden ba. Sai dai a ranar 26 ga watan Afrilun 2013 an sake dawowa da cheque din kuma an fitar da kudaden.
" Kotun ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranakun 20, 21 da 22 na watan Mayun 2019 karkashin jagorancin alkaliyar kotun, Ijeoma Ojukwu.

No comments:
Write Comments