Thursday

Home "Ya zama Dole ku biya N30,000" : Cewar Shugaban NLC zuwa ga Gwamnoni
Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta sha alwashin sanya duk gwamnonin Najeriya a gaba har sai sun biya naira dubu talatin a matsayin mafi karancin albashi na ma’aikata, Sannan zasu saka kafar wando daya da duk gwamnan daya gaza biyan albashin.
kungiya kwadago, NLC Nigeria

Shugaban kungiyar kwadago na NLC, Ayuba Wabba ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu yayin da yake kaddamar da wani katafaren gidan yan fansho a garin Ibadan na jahar Oyo, inda ya bayyana shuwagabannin gwamnati a matsayin makiyan ma’aikata.

KU KARANTA: Wata sabuwa a Kannywood : Mustapha Naburaska ya maka Hadiza gabon a kotu  

Wabba wanda ya samu wakilcin shugaban kungiyar kwadago ta jahar Oyo, Waheed Olojede ya kaddamar da gidan yan fanshon dake dauke da dakin taro mai daukar mutum dubu daya,  karamin asibiti don kulawa da yan fansho, gidan rediyo, da kuma cibiyar kimiyya da fasaha.

“Mun gode wa Allah daya kawo mu karshen wannan gwagwarmaya ta karin albashi wanda muka fara tun shekarar 2011 har zuwa ranar Alhamis da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattafa hannu akan dokar, wanda hakan yasa dole ne duk wani mai daukan aiki ya biya ma’aikatansa N30,000 a matsayin karancin albashi.

“Sai dai abin haushin shine shuwagabannin gwamnatoci a kowanni mataki makiyan ma’aikata ne, ba kasafai suka fiya son bin umarnin dokar dake kula da walwalar ma’aikata ba, amma tunda har mun samu nasarar N30,000 zamu tabbata kowanni gwamna ya biya” Inji shi.

Daga karshe Wabba yace tare da kungiyar gwamnonin Najeriya aka cimma wannan sabon dokar karancin albashin, don haka ba zasu sassauta wajen gwagwarmayar ganin sun sauke nauyin dake rataye a wuyansu ba.
No comments:
Write Comments