Sunday

Home Yadda farfelar jirgin sojin sama ta hallaka babban soja mai suna Umar
Dakarun sojin sama dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Borno sun yi babban rashi bayan fankar jirginsu na yaki mai saukar ungulu tayi sanadiyar mutuwar wani babban jami'in soja mai mukamin 'air chief marsahal' da aka bayyana sunasa a matsayin Umar.
badakare ya mutu

Wani daga cikin matuka jirgin da abin ya faru a kan idonsa ya shaidawa jaridar TheCable cewar lamarin ya faru ne a garin Bama a yammacin ranar Asabar.
Hakan ta faru ne bayan jirgin ya samu matsala.

Top3

Marigayin, wanda ya kasance daya daga cikin matuka jirgin, ya fita ne domin dauko jakarsa, amma yayin da yake wuce wa ta jikin fankar jirgin sai ta fille masa kai, kuma nan take ya fadi matacce.

DUBA WANNAN: Bayan matsin lamba, Buhari ya yi magana a kan matsalar tsaro a Zamfara.
" Nan take farfelar jirgin dake aiki ta fille masa kai. Mun samu nasarar tashin jirgin, mun kuma mayar da shi sansanin mu. Babu alamar lalacewa a jikin fankar jirgin ," a cewar majiyar.

Wannan iftila'i ya afka wa marigayin da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Asabar.
Majiyar ta kara da cewa tuni aka sanar da iyalin marigayin, sannan ya kara da cewa ana shirin binne gawar sa.

Yadda farfelar jirgin sojin sama ta hallaka babban soja mai suna Umar Read more: https://hausa.legit.ng/1231956-yadda-farfelar-jirgin-sojin-sama-ta-hallaka-babban-soja-mai-suna-umar.html
No comments:
Write Comments