Friday

Home Zalunci: Shugaban Makaranta ya kone wata 'Daliba kurmus bayan ta tona masa asiri
Mutuwar wannan budurwa mai shekaru 19 kacal a duniya, Nusrat Jahan Rafi, ya haifar da mummunar zanga-zanga a yankin kasar dake nahiyyar Kudancin Asia. Firai Ministan kasar, Sheikh Hasina ya sha alwashin hukunta dukkanin masu hannu cikin wannan zalunci.
tearcher burned his student in Bangladesh
Bayan da masu hannu cikin wannan muguwar aika-aika sun gaza samun biyan bukata yayin da suka nemi Nusrat ta janye korafin keta mata haddi, sun yi mata wanka da makamashi na Kalanzir kuma suka kone kurmus.


Hukumar 'yan sanda yayin karin haske dangane da wannan lamari na takaici ta bayyana cewa, ta samu nasarar cafke mutane 17 ababen zargi inda daya daga cikin su ya amsa laifi sa da cewa sun aikata hakan ne bisa umurni na shugaban makaranta.

Babban jami'in dan sanda mai gudanar da bincike a kan wannan mugun ji da mugun gani, Muhammad Iqbal, ya shaidawa manema labarai na jaridar AFP cewa, Nusrat ta riga mu gidan gaskiya a ranar 10 ga watan Afrilu inda ba ta gushe ba wajen ci gaba da bayyana koke a kan shugaban makarantar da ya keta mata haddi.

KARANTA KUMA: Hattara! : "Yan ta'addar jihar zamfara sun fara kaura suna shiga wasu jahohi.

Jagorar kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasar, Meenakshi Ganguly, yayin babatu na neman a tabbatar da yiwa Nusrat adalci tare da nema mata hakki, ta kuma bayyana yadda gwamnatin kasar Bangladesh ta gaza ta fuskar kare al'umma daga cin zarafi.

SOURCE LEGIT. NG
No comments:
Write Comments