Friday

Home Ba zan iya komawa kauyenmu ba saboda matsalar tsaro –Cewar wani dan majalisa -
Wani dan majalisar wakilai daga jahar Neja, Abubakar Chika Adamu ya bayyana cewa sama da shekara daya kenan baya iya zuwa kauyensu balle ma ya kwana sakamakon yawaitan hare haren yan bindiga, daya samu asali daga tabarbarewar tsaro a yankin.

Abubakar Chika Adamu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Chika ya bayyana haka ne yayin zaman majalisar na ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu, inda ya koka kan halin matsanancin rashin tsaro da jama’ansa ke fama dashi, wanda hakan yasa baya samun kwanciyar hankali.

Atiku ya haramta naira dubu goma goma da Buhari ke rabawa na Trader Moni

“Ya Kaakakin majalisa, ina zamu je ne? bana iya zuwa kauyenmu don na kwana, balle kuma nayi barci a yanzu, kimanin shekara guda daya kenan cur bana zuwa kauye, bana samun kwanciyar hankali a can, wannan shine mawuyacin halin dana tsinci kaina a ciki, ya zama wajibi mu dauki mataki.” Inji shi.
KU KARANTA:  Gwamnan Kano Ganduje ya fadi matsayar sa a kan sabon mafi karancin albashin ma'aikata.

Haka zalika wasu yan majalisu da suka fito daga yankin Arewacin Najeriya sun bayyana kokensu game da tabarbarewar tsaro daya addabi yankin, tun daga garkuwa da mutane, harin yan bindiga, rikicin Fulani da makiyaya da sauransu.
Wani dan majalisa daga karamar hukumar Safana, Ahmad Safana yace

“Hare haren da ake kaiwa a mazabata ya kazanta, duba da yadda maharan ke kashe mutane babu kakkautawa, tare da kona gidajensu, kuma su yi awon gaba da wasu.”

Shima dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Minjibir ta jahar Kano, Bashir Baballe ya koka da cewa

“Jama’a na neman mafita ne game da wannan matsalar tsaro da ake fama dashi, ya Kaakakin majalisa, jama’a basu iya zuwa kasuwannin kauye, don kasuwanci da zumunci ya rushe.”

Bayan sauraron korafen korafen yan majalisun, majalisar ta yanke shawarar gayyatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gurfana gabanta don tsatstsage mata bayani game da kokarin da yake yin a shawo kan matsalar.

MAJIYA : LEGIT.NG
No comments:
Write Comments