Wednesday

Home Bidiyo da hotuna : Bikin shan rantsuwar shugaban kasa da mataimakinsa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya a karo na biyu a yau Laraba, 29 ga watan Mayu.

Shugaban alkalan Najeriya, Justis Mohammed Tanko ne ya rantsar da shugabannin biyu.
Shugaba buhari yasha rantsuwa
Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ma ya isa dakin taro na Eagle Sqare.

A yanzu haka, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Oinbajo ya dauki rantswar kama aiki a karo na biyu.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a lokaccin da ake rantsar da shi
Farfesa Shehu Galadanci ne zai bude taron rantsa da shugabannin da addu'ar addinin Musulunci.

Yemi osinbajo ma ya sha rantsuwa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa dandalin Eagle Square da ke Abuja, inda za a rantsar da shi tare da Mataimakinsa Yemi Osinbajo a wa'adin mulki na biyu.

Tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Yakubu Gowon da tsohon Shugaban kasa, Cif Ernest Shonekan na daga cikin manyan mutanen da suka isa filin taro na Eagle Square a Abuja, wajen bikin rantsar da Shugaban kasa a yau Laraba, 29 ga watan Mayu.

 An rantsar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo a wajen taron.

Ga bidiyon anan.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa har yanzu tsoffin Shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Ibrahim Badamasi Babangida basu hallara ba a wajen taron.

KARANTA KUMA : Babban Dalilin da yasa sarki sunusi II bai halarci rantsuwar Ganduje ba.   

Sauran manyan mutanen da suka hallara sun hada da mambomin kungiyar sojojin diflomasiyya, manyan yan kasuwa, Aliko Dangote, gwamnoni, jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yan majalisa da sauransu.

An tattaro cewa an tsaurara matakan tsaro a wajen taron.
No comments:
Write Comments