Monday

Home Daga dawowarsa : Buhari ya yi jawabi kan harkan tsaro
Bayan dawowarsa shugaba Buhari ya zanta da manema labarai da suka so jin ta bakinsa akan yawan garkuwa da mutane, fashi da makami, yan bindiga da harin ta’addanci a kasar.

Sai dai, a lokacin da ya tsaya domin basu amsar wasu daga cikin tambayoyinsu, musamman wadanda suka nuna damuwa kan kafa sabuwar majalisarsa, Buhari yace, “Ba zan fada maku ba.”

Sai dai kuma, bayan yaki amsa sauran tambayoyin, an nemi ya amsa tambaya kan yawan sace-sacen mutane a kasar, amma sai yace “na lura mukaddashin sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu ya rairaye, koda dai wannan alamu ne nacewa yana aiki sosai."

KU KARANTA KUMA: Yadda farashin kayan masarufi suka kasance yayin da ake gab da shiga watan Azumi.  

Shugaba Buhari ya samu tarba daga shugaban ma’aikatansa, Abba Kyari, ministan birnin tarayya, Muhammed Bello; shugaban hafsan soji, Tukur Buratai, mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu da wasu hadimansa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Fadar shugaban kasa ta bukaci 'yan adawa da masu hamayya da gwamnatin tarayya da su janye kalamansu da suka yaudari wasu 'yan Najeriya da shi a kan cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar Ingila ne domin a duba lafiyar sa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan wata ziyara ta 'kashin kan sa' da ya kai zuwa kasar Ingila.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments