Sunday

Home Gaskiyar Abin Da Yasa Gwamna Ganduje ke Yakar Sarki Sunusi II.
Tun bayan fitowar maganar kirkirar sabuwar dokar masarauta a jihar Kano, jama'a suka fara bayyana cewar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na shirin yakar sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a kan dalilan da ba a gama hakikance su ba, duk da dai wasu sun ce yin hakan na da alaka da siyasa.

Ganduje and Sunusi
                           Ganduje and sarki Sanusi II


Yanzu haka bayanai na gaskiya sun fara bayyana a kan dalilan da yasa Ganduje ya tsaga gidan sarautar Kano har gida biyar.
Wata majiya dake da kusanci da gwamnatin jihar Kano ta shaida wa majiyar mu cewar gwamna Ganduje na da masaniyar cewar sarki Sanusi II ya gana har sau biyar da jagoran siyasar gidan Kwankwasiyya, tsohon gwamna kuma sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da kuma dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), domin tsara yadda za a kayar da gwamnatin Ganduje.


Daya daga cikin majiyar ta bayyana cewar sarki Sanusi II ya umarci hakimai da su goya wa jam'iyyar PDP baya a zaben gwamna da kuma tabbatar da cewar jam'iyyar APC ta fadi a zaben gwamnan jihar Kano.

"Har 'yan uwansa ya tattara ya sanar da su cewar su yi aiki tare da jam'iyyar PDP domin tabbatar da cewar gwamna mai ci bai samu damar yin tazarce ba. Ba iya nan fa ya tsaya ba, sarkin ya yi amfani da kujerar sa wajen tara wa jam'iyyar PDP kudi masu yawa daga wurin abokan kasuwancin sa domin tayi yakin neman zabe duk don a kayar da Ganduje ," a cewar wani jami'in gwamnatin jihar Kano.
Majiyar gwamnatin ta kara da cewa bayan an bayyana cewar zaben gwamnan jihar Kano bai kammalu ba, sarki Sanusi ya tuntubi fadar shugaban kasa, uwar jam'iyyar APC ta kasa da shugabannin hukumomin tsaro domin ganin cewar ba a sake gudanar da zaben kece raini a jihar Kano ba, bisa nuna cewar jama'a sun riga sun zabi Abba, dan takarar jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Hanyoyin da Dangote ya bi ya hana Ganduje tsige Sarkin Kano
" Ya fada musu cewar za a iya samun barkewar rikici a jihar Kano matukar ba a bayyana Abba Yusuf, dan takarar jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben ba. Amma bayan ya ga cewar ba za a fasa gudanar da zaben raba gardama a wasu mazabu ba, sai ya canja dabara, ya koma zuga shugabannin hukumomin tsaro a jihar Kano domin kar su bari APC ta samu nasara ," a cewar majiyar.

Majiyar ta ce dukkan wadannan abubuwan da Sanusi ya yi ba boyayyu bane a wurin gwamna Ganduje kuma su ne suka fusata shi har ta kai ya dauki matakin da ake ta cece-kuce a kai.
Da aka tuntubi kwamishinan yada labaran gwamnatin Kano, Malam Muhammad Garba, domin tabbatar da wannan labari, ya ce bashi da ta cewa a kan dangantakar da take tsakanin sarki da gwamna, tare da bayyana cewar " an riga an kirkiri sabbin masarautu ."

Da aka tuntubi shugaban ma'aikatan sarki, Alhaji Munir Sanusi, ya ce bashi da hurumin yin magana a kan batun, tare da bayyana cewar, " ba ni da hurumin yin magana da manema labarai a kan wannan batu saboda akwai na sama da ni da dama a tsarin fada."

POSTED-BY LEGIT.NG 
No comments:
Write Comments