Saturday

Home Hanyoyin da Dangote ya bi ya hana Ganduje tsige Sarkin Kano
Marigayi tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I wanda ya yi mulkin shi daga shekarar 1905 zuwa 1990, kaka ga Sarkin Kano na yanzu, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, ya yi mulki na shekaru biyar ne kawai, daga baya aka takura shi akan sai ya yi ajiye mulkin. An ce Sarkin ya kasance bai iya gabatar da mulki ba saboda yawan son shiga harkar siyasa da yake dashi, hakan ne ya sanya dole aka cire shi daga mulkin.

Ganduje sunusi Dangote

Alamu sun nuna cewa Sarkin na yanzu, Muhammadu Sanusi II shi ma yana fuskantar irin wannan yanayi, inda gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya nuna rashin jin dadin sa akan wasu abubuwa da ya ke yi a jihar.

Hakan ne ya tilasta gwamnatin jihar kirkirar wasu sababbin masarautun yanka guda hudu wadanda za su ragewa Sarkin Kano matsayi a jihar, bayan gwamnan jihar ya aika da dokar gurin majalisar jihar, majalisar ta amince da dokar inda aka kara sababbin masarautu guda hudu a fadin jihar. Wadanda suka hada da masarautar Bichi, Gaya, Karaye, da kuma Rano.
Wani abin mamaki kuma shine, babu wata kungiya, ko wani babba arewa ko fadar shugaban kasa da ta sanya baki akan lamarin, duk sun barshi ya ji da kansa.

Sai dai kuma, shahararren mai kudin nan na nahiyar Afirka Alhaji Aliko Dangote, shi ne kadai wanda ya shiga lamarin, inda ya roki gwamnan jihaar akan kada ya cire Sarkin daga kujerar shi, amma Ganduje ya nuna dole sai ya cire shi.

KU KARANTA: Ya kashe mahaifinsa saboda ya hana shi Fita Yawo.  

Wata majiya daga gidan gwamnatin jihar ta ce Ganduje ya bai wa Dangote wasu ka'idoji da dole ne sai an cika su domin ceeto sarkin, tunda har sarkin ba zai daina zagin gwamnatinsa ba.

Majiyar ta ce, "Gwamnan ya gayawa Dangote ya je ya sanar da Sarkin cewa ya zabi abu daya a cikin guda uku da zai gindaya masa: ko ya yi murabus da kansa, ko kuma gwamnati ta cire shi da karfin tsiya, ko kuma gwamnati ta kirkiro wasu sababbin masarautun yanka guda hudu a jihar. Ganduje ya bayyanawa Dangote cewa dole zai aiwatar da daya daga cikin wadannan ka'idoji guda uku da ya gindaya, tunda har sarkin ba zai daina shiga harkar siyasar jihar ba. Amma ba dan Dangote ba da tuni Ganduje ya cire Sarkin daga kujerar shi," in ji shi.

Posted by LEGIT.NG

No comments:
Write Comments