Thursday

Home Jerin Gwamnoni 12 da suka bar karagar mulki sakamakon zaben 2019
Akasarin gwamnoni sunyi nasarar kammala wa'adin mulkin shekara 8 kamar yadda yake acikin kundin tsarin dokokin Najeriya.

Gwamnoni 12 ne suka sauka daga kan mulkin jihohinsu a jiya bayan wasu daga cikinsu sun kammala wa’adin mulki na shekara 8 kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tsara.

Da dama daga cikinsu wadanda suka cika wa’adin mulkin nasu na shekara 8 da ma wadanda suka sha kasa bayan sunyi wa’adi guda daya kacal sun mika karagar mulki zuwa ga sabbin gwamnoni domin cigaba daga inda suka tsaya.

KU KARANTA: Bidiyo da hotuna : Bikin shan rantsuwar shugaban kasa da mataimakinsa.

Gwamnonin da suka yi murabus sun hada da.

Rochas Okorocha - jihar Imo.

Akinwunmi Ambode - jihar Legas.

Ibikunle Amosun - jihar Ogun.

Kashim Shettima - jihar Borno

Jibrilla Bindow - jihar Adamawa.

Abubakar Bello - Jihar Neja.

Muhammad Abdullahi Abubakar - Jihar Bauchi.

Abdulfatah Ahmed - Jihar Kwara

Umaru Tanko Al-Makura - Jihar Nasarawa.

Ibrahim Danwambo - Jihar Gombe.

Abdulaziz Yari - Jihar Zamfara.

Ibrahim Gaidam - Jihar Yobe.

Sabbin gwamnoni wadannan jihohin su ne:

Ahmadu Fintiri (PDP, Adamawa).

Bala Muhammad (PDP, Bauchi).

Babagana Zulum (APC, Borno).

Inuwa Yahaya (APC, Gombe)

Emeka Ihedioha (PDP, Imo)

Abdulrahman Abdulrazaq (APC, Kwara).

Babajide Sanwo-Olu (APC, Legas).

Abdullahi Sule (APC, Nasarawa).

Dapo Abiodun (APC, Ogun).

Seyi Makinde (PDP, Oyo).

Mai-Mala Buni (APC, Yobe).

Bello Matawalle (PDP, Zamfara).
No comments:
Write Comments