Wednesday

Home Kannywood: Kotu ta janye dokar kama wata shahararriyar yar fim din Hausa da ta bayar a baya
Gabon ta karyata cewa ta roki jarumi Nabaraska.

Image© bbc


Kotun majistare wacce ke garin Kano ta janye dokar da ta bayar ga kwamishinan ‘yan sanda na ya kamo Hadiza Aliyu Gabon.
Idan bamu manta ba Mustapha Badamasi wanda aka fi sani da Nabraska shine yayi karar jarumar akan zargin taci zarafinsa.

KU KARANTA: Kwana Casa'in - Kashi Na bakwai 7- AREWA24.   

Bayan Nabraska ya shigar da karar jarumar zuwa kotun majistare dake Kano, sai kotun ta aikawa Hadiza da sammaci yayin da taki bayyana a gaban kotun.

Shugaban wannan kotun, Muntari Dandago shine ya baiwa kwamishina Muhammad Wakili umarnin a kamo masa wannan jaruma saboda taki amsa gayyatar kotu.

A wani labari mai kama da wannan, Hadiza Aliyu Gabon ta karyata labarin da ake yadawa a kanta na cewa wai 'yan sanda sun kamata sannan kuma ta durkasa har kasa domin neman afuwar Nabraska.

Jarumar tayi watsi da wannan labari inda take cewa, " Babu dan sandan da ya kama ni, kuma ni da Mustapha mun yi sulhu ne a harabar kotu amma ban durkusa ma kowa ba. Masu yada wannan labari suna kokarin bata min suna ne kawai." 

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments