Wednesday

Home › › Katankatana! Rikicin masarautar Kano ta dauki sabon salo, manyan hakimai 4 sun yi tirjiya
Manyan hakiman fadar Sarkin Kano guda hudu wadanda hakkin zaben Sarki a masarautar Kano ya rataya a wuyansu sun nuna ma Ganduje yatsa game da raba masarautar Kano, inda suka garzaya gaban kotu domin kotu ta dakatar da gwamnan.
Sarki sunusi
Sarki Sunusi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito manyan hakiman sun hada da Madakin Kano Yusuf Nabahani, Makaman Kano Sarki Ibrahim, Sarkin Dawaki maituta, Bello Abubakar da kuma Sarkin Bai, Mukhtar Adnan hakimin Dambatta.

KU KARANTA: Tirkashi : Dogaran Sarkin Kano sun fara gudu daga fadar Kano. 

Hakiman sun shigar da wannan kara ne gaban babbar kotun jahar Kano inda suke karar gwamna jahar Kano, kaakakin majalisar dokokin jahar, majalisar dokokin jahar, gwamnatin jahar Kano, kwamishinan shariar jahar da kuma sabbin Sarakuna masu daraja ta daya da Ganduje ya nada.

Hakiman sun nemi kotu ta haramta wannan nadi da Ganduje yayi duba da cewa sune masu ikon zaban sabon Sarki a masarautar Kano, kuma wannan nadi da yayi yayi kaca kaca da tarihin sarautar Kano, kuma ya bata musu aiki, musamman duba da cewa sune wakilan gidajen Jobawa, Sullubawa, Yolawa da Dambazawa.

KARANTA WANNAN : Kwana Casa'in - Kashi Na Shida 6 - AREWA24.   

Domin su nuna da gaske suke a wannan shari’ar, manyan hakiman sun dauki hayar manyan lauyoyi masu lambar SAN guda bakwai da suka hada da Lateef Fagbemi, AB Mahmoud, Adeniyi Akintola, Paul Usoro, Suraj Sa’eda, Hakeem Afolabi da Nassir Dangiri.
Rikicin kano
Takardar kara

Sai kuma wasu kananan lauyoyi guda goma sha bakwai da suka hada da Maliki Kuliya, Nureini Jimoh, Nasiru Aliyu, Muritala Abdulrasheed, Aminu Gadanya, Ismail Abdulaziz, Sagir Gezawa, Rashidi Isamotu, Oseni Sefiullahi, Ibrahim Abdullahi, Haruna Zakariyya, Auwal Dabo, Badamasi Suleiman, O.O Samuel, Fariha Sani Abdullahi, Yahaya Abdulrahseed da Amira Hamisu.

News SOURCE Legit.Ng
No comments:
Write Comments