Friday

Home Sharhin Fim Din FAN

Fan indian movie 2016

Fan Fim Din Bollywood ne da aka fitar a shekara ta 2016, kuma wannan Fim yana dauke ne da labarin wani masoyin babban jarumin Fina Finan India inda har soyayya ta kan juya ta zama Kiyayya.
fan indian movie 2016
fan indian movie 2016

An Fitar Da wannan Fim ne a Ranar 15 April 2016, kuma an kashewa Fim Din kudi kimanin Miliyan
850, Fim Din ya kawo kudi kimanin Biliyan ₹1.2 a India sannan ya kawo Miliyan ₹679 a Kasuwancin duniya baki daya.

* Bada Umurni = Maneesh Sharma
* Daukar Nauyi = Aditya Chopra
* Tsara Labari = Habib Faisal
* Labari = Maneesh Sharma
* Jarumin Fim = Shah Rukh Khan
* Sautin Waka = Vishal–Shekhar
* Taken Fim = Andrea Guerra
* Tacewa = Namrata Rao
* Kamfanin Da Ya Shirya = Yash Raj Films
* Lokaci = Mintuna 138
* Kasa = India
Harshe = Hindi

LABARIN FIM DIN

Gaurav Chandna (Shah Rukh Khan ) Dan a mutun masoyin wani Jarumin Fina Finan Bollywood ne mai suna Aryan Khanna (
Shah Rukh Khan ). Yana son Neha, Abokiyar sa kuma Makwabciyar sa.
Fuskar Gaurav tana Matukar kama da fuskar Aryan, Hakan ya taimake shi wajen lashe kambun Gasar wasan Kwaikwayon da ake yi a Delhi ta hanyar Kwaikwayon Aryan.

Bisa samun kwarin Guiwa da kuma yardar iyayen sa, sai Gaurav ya hau Jirgin kasa daga Delhi zuwa Mumbai ba tare da ya sayi tikiti ba don yaje ya Nunawa Aryan lambar yabon da ya samu a Sanadiyyar soyayyar da yake masa.
Bayan ya isa Mumbaai, sai Sid Kapoor (Taher Shabbir Mithaiwala), Matashin jarumin Fim ya Bayyanawa Kafafen watsa Labarai rashin jin dadin wasu abubuwa da shi Aryan din yake yi. Hakan yasa Gaurav ya Harzuka har ta kai ga ya dake shi kuma ya Tirsasashi akan sai ya bada hakuri Yayinda shi kuma yayi Rikodi na bada Hakurin. Nan da nan Bidiyon ya hau kan Yanar gizo, shi kuma Aryan sai ya sa aka kama Gaurav.

Bayan an kama shi an kulle, sai 'yan Sandan ofishin suka Zane shi, daga nan kuma sai Aryan din da kanshi yazo ya ziyarce shi, cikin nuna bacin rai Aryan ya bayyana mishi cewa shi ba Masoyin sa bane kuma shi yasa aka kama shi.
Cikin Sagewar Guiwa Gaurav ya dawo gida, ya kona duk wani abu na jarumin kuma ya sha Alwashin cewa sai ya dau fansa akan Aryan tunda dai ya juyawa babban Masoyinsa baya.

Shekara daya bayan faruwar hakan, Gaurav sai ya tafi Landan ya shiga gidan Tarihin adana mutum mutumi na Madame Tussauds wax museum, a matsayin Aryan kuma ya tada hayaniya a wurin. Shi kuma Aryan din na asali sai aka kama shi aka kulle, daga baya dai aka bada belin sa inda ya tafi Dubrovnik domin ya gabatar da wani taro. A nan ne Gaurav ya kira shi ya bayyana masa cewa shi ne ya jawo mishi wannan rigimar kuma in bai bashi hakuri ba bazai daina takura masa ba. Aryan shi kuma sai yaki bada Hakurin. Hakan yasa Gaurav yayi shiga irin ta 'Yantawagar Aryan domin yaje wannan taron.

Aikin dake gaban Aryan na gaba shi ne zuwa bikin wata 'yar wani hamshakin mai kudi a Croatia. A can ne yaga an aiko masa da Kati mai dauke da sakon "Say sorry," hakan yasa ya fahimci cewa Gaurav yazo wajen. Shi kuma Gaurav sai yayi basaja a matsayin Aryan ya Ciwa Amaryar da aka zo bikin nata zarafi.
Ita kuma amarya sai ta ji Haushi harta yiwa Aryan din rashin mutunci ta kore shi. Bayan ya fito, sai Aryan ya hangi Gaurav, don haka sai ya bishi amma ya sha da kyar bai samu kama shi ba. Wannan Abu kuma da ya faru da amarya sai nan da nan ya karade ko ina akayi ta Zagin Aryan ana kin zuwa tarukansa da kallon Fina Finan sa.

A can kuma India, Gaurav sai ya tafi gidan Aryan Ya Farfasa masa lambobin yabon sa. Shi kuma Aryan sai ya nufi gidan su Gaurav ya same su tare da Neha. Daga nan sai ya tsara wani shiri tare da iyayen Gaurav da kuma ita Neha din domin ya Kwaikwayi Gaurav. Haka kuwa aka yi, Aryan ya fito filin wasan Kwaikwayon a matsayin Gaurav harma yana Baiyanawa duniya irin son da yake yiwa Neha. Wannan al'amari sai ya batawa Gaurav rai har ya harbi Aryan da bindiga.

Aryan sai ya bishi domin ya kama shi. A garin haka ne suka yi damben mutuwa inda daga karshe dai Aryan ya nemi Gaurav da ya daina Kwaikwayon sa ya ci gaba da rayuwar sa salin Alin. Shi kuma Gaurav sai ya bayyana masa cewa ai ya riga ya Lalata masa rayuwa kuma ya tuna masa da cewa har yanzu fa bai bashi hakurin da ya nema ba. Daga nan Gaurav ya fada kasa daga saman bene yana mai yin murmushi a yayin mutuwar sa.

Bayan Faruwar wannan al'amarine komai ya dawo wa Aryan daidai inda aka wanke shi tas! Daga dukkan wani zargi, sai dai wannan al'amari yana ta damunshi a Zuciyar sa. Yayinda bikin Maulidin Aryan ya zagayo, lokacin da ya fito domin ya gaisa da masoyan sa, sai Aryan ya dinga ganin Gaurav yana masa gizo tare da yin Murmushi.

JARUMAN FIM DIN

* Shah Rukh Khan = Aryan Khanna / Gaurav Chandna
* Waluscha de Sousa = Bela Khanna
* Sayani Gupta = Sunaina Khanna
* Shriya Pilgaonkar = Neha
* Deepika Amin = Mahaifiyar Gaurav
* Yogendra Tiku = Mahaifin Gaurav
* Taher Shabbir Mithaiwala = Sid Kapoor
* Parveen Kaur
* Chandru Bhojwani = Raj
* Indraneel Bhattacharya = Akhtar
* Zachary Coffin
* Megha Gupta = Payal

Waka daya akayi domin ta fito a cikin Fim Din, ita ma daga baya aka cire ta. Sai dai wannan Fim ya samu Yabo sosai a wurin jama'a musamman irin kokarin da akayi wajen maida Jarumi Shah Rukh Khan karamin yaro Matashi Alhalin ya haura shekaru hamsin. Kuma an yabawa jarumin sosai wajen irin yadda ya baiwa kowane aiki hakkkinsa a cikin wannan Fim. Sannan wannan Fim ya samu shiga cikin Jerangiyar Fina Finan India Wadanda ba za'a taba mantawa da su a Tarihin Masana'antar Fina Finan India ba, domin Fim ne da ba'a taba yin kwatankwacin sa ba. Duk da cewa bai yi abin azo a gani a kasuwancin Fina Finai na gida ba, fim ɗin ya taka rawar gani a ƙasashen waje.
No comments:
Write Comments