Saturday

Home Wani likita ya makala wa manya 25, da yara 65 cutar kanjamau
A kalla mutane 90, da suka hada da kananan yara 65, anka tabbatar da wani likitan dake dauke da cutar kanjamau ya makala masu cutar, a kasar Pakistan, ta hanyar yin amfani da sirinjin allurar da ya gurbata, kamar yadda jami’ai suka ce a ranar Jumu’a.

kiwon lafiya

“Mun kama wani likita bayan mun karbi korafe-korafe daga hukumomin lafiya” In ji Kamran Nawaz, wani jami’in ‘yansandan dake jagorancin sharia’r a kudancin birnin Larkana.

Jami’in ‘yansandan yace:
“An fada muna cewa likitan na dauke da cutar kanjamau”
An fara fadakar da hukumomi gameda al’amarin a makon da ya gabata bayan da aka samu yara 18 dauke da cutar kanjamau sakamakon jaraba su da aka yi, wanda ya karfafa ma jami’an lafiya da su gudanar da cikakken bincike.

An gano karin masu dauke da cutar da yawa.
“Sama da mutane 90 aka samu dauke da cutar, kuma yawan kananan yara ya kai 65,” Kamar yadda wani jami’in lafiyar gunduma mai suna Dr. Abdul Rehaman, ya fada ma kamfanin dillancin labaran AFP.

Wani jami’i ya tabbatar da wannan annobar, kodayake ya bada bayani daban kan yawan mutanen da abun ya shafa.
Hukumomi sunce sun bi diddigin abunda ya faru inda suka samu wani likitan da hannnu dumu-dumu, wanda yake amfani da gurbataccen sirinjin allura kan maras lafiya.

Azra Pechuho, Ministan lafiyar yankin ya tabbatar da kama likitan.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Yakubu Gowon ya yanke jiki ya fadi a wajen jana’iza a jihar Delta.     

“Kuma an jarraba jinin iyayen yaran da abun ya shafa, amma ba a same su da cutar ba”      In ji Pechuho.

Tuni jami’ai suka dukufa wurin gagarumin shirin binciken jini da ilmantar da mutane.
Ana ganin kasar Pakistan a matsayin kasar dake da karancin yaduwar cutar kanjamau, amma cutar na fadada mafiyawanci a tsakanin masu amfani da alluran da ake yi a jijiyoyi, karuwai da leburorin da suka tafi aikin kwadago a yankin Gulf.

MAJIYA : LEGIT. NG
No comments:
Write Comments