Saturday

Home Ya kashe mahaifinsa saboda ya hana shi Fita Yawo
Saurayin ya yi amfani da addar da mahaifin ya dauko don tsorata shi ya farke mishi ciki
Hukumar 'yan sandan jihar Ogun ta kama wani matashi mai suna Babatunde Olagesin, da laifin kashe mahaifinsa, mai suna Taiwo Olagesin, inda ya yi amfani da adda, bayan sun samu sabani tsakaninsu a yankin Ijoko da ke jihar ta Ogun, ranar Litinin 6 ga watan Mayu.


A rahoton da muka samu, rikcin ya samo asali lokacin da Babatunde ya bukaci mahaifin nasa akan cewa yana s yaje Oshodi da misalin karfe 6 na safiyar ranar, mahaifin nashi ya hana shi fita daga gidan, inda ya ce mishi yana so suje unguwa tare.

Mahaifin ya rufe kofar gidan domin kada 'dan ya fita. Hakanne ya jawo rikici tsakanin su, inda suka kaure da fada. Hakan ya sanya mahaifin dauko adda domin ya tsorata dan nashi, shi kuma a kokarin da yake na ganin ya kwace addar daga hannun mahaifin nasa, sai yayi amfani da addar ya cakawa mahaifin nasa a ciki.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Dalilin da ya sa nake auri-saki | Adam Zango  

Mun samu rahoton cewa, makwabtansu ne suka sanar da hukumar 'yan sanda faruwar lamarin, inda a take jami'an 'yan sandan suka kama Babatunde.

A lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce nan ba da dadewa ba za su kai mai laifin zuwa kotu.

SOURCE  LEGIT.NG

No comments:
Write Comments