Friday

Home Yadda Rikici ya barke Tsakanin Matan Kannywood Biyu - Akan Dino Melaye
Duka 'yan matan sun yiwa Sanatan waka da fasta ta siyasa sun kai masa, inda ya dauki hoto da kowaccen su.

Wani rikici da ya barke tsakanin matan Kannywood guda biyu Teema Makamashi da Fati Mohammed, inda suke rikici akan Sanatan jihar Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye.
Rikicin ya samo asali ne lokacin da Teema Makamashi take gargadin Fati Mohammed akan kwaikwayenta da tayi wurin yiwa Sanatan waka.


Wata sabuwa: Rikici ya barke tsakanin matan Kannywood biyu akan soyayyar Sanata Dino Melaye
Ga abinda Teema Makamashi ta rubuta a shafinta na Instagram:

"Keda samun soyayyarsa sai dai ki gani daga nesa"

Tauraruwar Teema Makamashi wacce ita ce ta fara yiwa Sanata Dino Melaye waka, tayi wannan habaicin ne ga Fati Mohammed wacce ta kwafeta.

KU KARANTA: Bidiyo da hotuna : Bikin shan rantsuwar shugaban kasa da mataimakinsa.  

Teema tayi rubutun ne a shafinta na Instagram inda ta cigaba da cewa, "Ga wani sabon salon shima idan zaki yi, banda waka, tunda kome nayi sai kinyi, kina tare da bakar wahala indai ni zaki dinga kwaikwaya."

Tauraruwar ta saka hoton fastar siyasa da tayi wa Sanatan a shafinta na Instagram a lokacin da tayi wadancan habaicin.

An ga Fati Mohammed ta yiwa Sanata Dino Melaye waka da kumaa fasta ta siyasa.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments