VISIT US ON AREWASOUND.COM


HOTTREND ONLINE :
Music Mp3 - Sabuwar Wakar Hamisu Breaker mai suna - Bazana Manta Maryam Ba.
CHECK NEW PRODUCTS HERE
Hamisu breaker 2020 Album Download Mp3 music

Sammani aa 2020 Album : Download Complete Album (Akwai lokaci)

Umar M Shareef Zeenaru 2020 Official AUDIO+VIDEO

MUSIC: Melery 2020 Song Da Dadi So

Friday

Home Yanzu Yanzu: Yakubu Gowon ya yanke jiki ya fadi a wajen jana’iza a jihar Delta
Janar Yakubu Gowon, tsohon Shugaban kasar Najeriya ya yanke jiki ya fadi a lokacin jana’izan Manjo Janar David Akpodiete Ejoor a garin Ovwor-Olomu, karamar hukumar Ughelli ta kudu da ke jihar Delta.
yakubu gawon

Lamarin ya afku ne a gefen kabarin yayinda ake jawabi a jana’izar.
Wasu manayan sojoji sun yi gaggawan daukar tsohon Shugaban kasar zuwa wani rumfa na mussamman da aka tanada domin agajin gaggawa yayinda Gwamna Arthur Ifeanyi Okowa da Cif James Onanefe Ibori, tsohon gwamnan jihar Delta suka koma wajen don tabbatar da farfadowarsa.

Nan take aka turo motocin daukar marasa lafiya na jihar Delta zuwa gaban rumfar esaboda koda lafiyar tsohon Shugaban zai ci gaba da tabarbarewa.

KU KARANTA KUMA: Ba zan iya komawa kauyenmu ba saboda matsalar tsaro –Cewar wani dan majalisa -   

Bayan dan wani lokaci sai aka gano Cif James Onanefe Ibori da Gwamna Arthur Ifeanyi Okowa na fitowa daga rumfar na mussaman, wanda hakan ya nuna cewa tsohon Shugaban kasar ya farfado
No comments:
Write Comments