Monday

Home Zaben gwamna a Kano: Ganduje zai gabatar da kundi mai shafi 1,800 a gaban kotu
Ganduje ya shirya kundi mai dauke da shafi 1,800 kuma a shirye yake ya gabatar da shaidu 203 tare da su.

“Mun shirya don nuna ma duniya cewa tabbas an gudanar da zabe na gaskiya da adalci a ranar 23 ga watan Maris, 2019”, cewar lauyan shi Barista Musa Abdullahi Lawan.

KU KRANTA KUMA: Gaskiyar Abin Da Yasa Gwamna Ganduje ke Yakar Sarki Sunusi II.  

Yayin da yake magana bayan ya shirya takardun gwamnan a gaban kotun sauraran karan, Barista MA Lawan, wanda ya kasance daya daga cikin jagoran lauyoyin gwamnan, yace ikirarin da jam’iyyar PDP ta gabatar gaban kotun ba mai inganci bane.

Barista MA Lawan yace zasu gabatar da shaidu 203 wadanda suka kasance masu muhimmanci, zasu kuma fada ma kotun cewa tabbas an gudanar da zabe da kuma cewa jam’iyyar PDP ta gabatar da kara mara tushe.

Lauyan na Ganduje yayi watsi da rade-radin cewa jihar ta tayi amfani da damar yima alkalai sauyin wjen aiki domin shigo da wadanda zasu goya musu baya.

Ya kuma dage cewa akwai kararraki 50 a gaban kotun kuma yawancinsu sunyi ma kotun yawa.

SOURCE LEGIT.NG

No comments:
Write Comments