Friday

Home Zamfara: An ba hammata iska tsakanin magoya bayan APC da PDP a harabar kotun koli (bidiyo)
Wani bidiyo da ya billo a yanar gizo ya nuna yadda aka yi musayar naushi a tsakanin magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara.

Lamarin dai ya afku ne a yau Juma’a, 24 ga watan Mayu a harabar kotun koli, yayinda ake zartar da hukunci akan zaben jihar.
Rikicin dai ya kaure ne bayan an yamutsa gashin baki tsakanin matasan jam’iyyun biyu.

Ga bidiyon a kasa:


KU KARANTA KUMA: Kannywood: An Nemi Fansar Miliyan 10 Bayan Sace Mataimakin Shugaban MOPPAN 

Da farko dai Legit.ng ta rahoto cewa Kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar All Progressives Congress APC ba tada hakkin takara a zaben gwamnan jihar kuma saboda haka, an yi fatali da dukkan kuri'un da ta samu.

Gamayyar alkalai biyar na kotun sun yi ittifaki a ranar Juma'a cewa jam'iyyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ga ka'idojin jam'iyyar.

Babban alkali, Paul Adamu Galinji, ya ce dukkan kuri'un da aka kadawa jam'iyyar APC banza ne kuma sannan jam'iyyar da tazo na biyu a zabubbukan ne zababbun masu kujerar.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments