Tuesday

Home Ba za'a dauki lokaci mai tsayi wajen bayyana sunayen minstoci ba : shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi magana a game da shirin kafa gwamnatinsa a Najeriya. Hakan na zuwa ne bayan kusan wata guda da shugaban kasar ya sake darewa kan karagar mulki.

Shugaba Buhari ya yi wannan magana ne ta bakin babban Hadiminsa, Femi Adesina, wanda ya ce a wannan karo, shugaban kasar ba zai dauki dogon lokaci wajen fitar da sunayen Ministocinsa ba.

Femi Adesina ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya yi wata doguwar hira da Mujallar Interview Magazine. Mista Adesina ya yi wannan jawabi ne a Ranar Litinin dinnan, 24 ga Watan Yuni, 2019. A 2015, shugaban kasar ya dauki kusan rabin shekara ba tare da ya kafa gwamnati ba.

Wannan ya jawo jama’a su ka fara kiransa ‘Baba Go Slow’ watau da Hausa "Uban Masu nawa a Najeriya!"

DUBA WANNAN : Kwana Casa'in - Kashi Na Sha biyu 12 - AREWA24 

Da a ka tambayi Adesina game da lokacin da za a nada manyan mukarrabai a gwamnatin Buhari, sai ya ce jama’a ba za su kara kwana guda na lokacin da bai zama dole ba wajen jiran Ministoci. Mista Adesina ya ce: “Shi kan sa shugaban kasa ya fada da bakinsa cewa wannan karo ba za a jima wajen kafa gwamnati kamar yadda a ka yi a 2015 ba, dalili kuwa saboda yanayin ba daya ba ne.”

A wancan lokaci a wa’adin farko, fadar shugaban kasar ta kowa da cewa an samu bacin lokaci wajen mikawa gwamnati mai zuwa wasu takardu wanda hakan ya yi sanadiyyar dadewar da a ka yi. Idan ku na biye da mu, ku na da labari cewa har yanzu babu wadanda shugaban kasa ya nada face Akanta Janar na kasa da kuma shugaban kamfanin NNPC tun da ya zarce a kan mulki a Watan Mayu.
No comments:
Write Comments