Wednesday

Home Bayani Akan Sabon Tsarin Startup Nigeria Program 2019
Tallafin jari haɗin guiwa da ofishin vice president.

Startup Nigeria Program 2019


Startup Nigeria Program 2019, How to Apply Startup Nigeria Program 2019, Startup Nigeria Signup

Wannan wani Sabon tsari ne na tallafawa ƴan Nigeria ta yadda zasu bude masana'antu domin tallafawa kawunansu da kuma al'umma wanda ofishin mataimakin shugaban kasa professor yemi osinbajo ya fitar.


SHIN NA CANCANTA NAYI APPLY NA Startup Nigeria Program ?

Eh babu shakka wannan tsari na dukkan wani ɗa Nigeria ne , kuma Shi wannan program da akayiwa laƙabi da (2019 Startup Nigeria Program) Za'a gabatar dashi ne a sassan Nigerian wanda ya haɗa da North West, North Central da South East.

Jihohin da suke a North West Sun haɗa da : Jigawa, Katsina, Kaduna, Kano, Kebbi, Sokoto Zamfara.

Wanda suke a North Central sun haɗa da Niger, Kwara, FCT, Benue, Kogi, Plateau, Nasarawa

Na South East kuma sune Imo, Anambra, Enugu, Abia, Ebonyi

Menene zan samu daga StartupNigeria?

Wanna program anyi shine don ƴan Nigeria kawai, musamman matasa waɗanda suka fara kasuwanci, kaɗan daga ciki amfanin wannan program (Startup Nigeria) sun haɗa da.

Horo : An tsara Shirin Shirye-shiryen don taimakawa ƙananan kamfanoni da ƴan kasuwa don su tabbatar da maganganunsu.

Gudanarwa: Shirin zai ba ku damar saduwa da ƙwararru don inganta harkokin kasuwancin da kuma taimaka wa 'yan kasuwa don su yi nasara a harkokin su na kasuwanci.

A ƙarshen Shirin, Waɗanda suka halarci wannan training zasu karɓi jari don taimakawa wajen kawo ra'ayoyinsu da tallafawa a nan gaba. Za a ba da jarin kai tsaye ta asusun kuɗin ku. (Bank Account)

LOKACIN FARA YIN REGISTER
Wannan Program zai dinga tafiya ne a shirye kamar yadda aka tsara, Za'a fara yin register online daga ranar 27-may-2019 , za'a rufe rananr 17-june-2019.

Sannan za'a shirya training na musamman ga waɗanda suka samu nasarar shiga wannan program a ranar 8th da 26th - July- 2019.

How to Apply Startup Nigeria Program 2019

Application Process
Gabaɗaya process da akebi don yin register a wannan program ana yinshi ne online.
Note : Kar wani yace maka yana siyar da form ko wata takarda, kai tsaye shiga ake ciki shafinsu sai a cike abun da ake buƙata don yin register, wannan shine shafin su kai tsaye  Startups Nigeria Program🔗, Bayan kashiga zaka Amsa tambayoyi don shiga sahun waɗanda suke sa ran samu nasara.

Kana buƙatar wani ƙarin bayani game da Startup Nigeria 2019? Zaka iya kasancewa dasu a shafukan su na social media don jin me yake gudana game da wannan program.

- Email: hello@startupnigeria.ng

- Twitter:&n6bsp;https://twitter.com/startsng

- Facebook: https://www.facebook.com/startsng

-  Instagram:https://www.instagram.com/startsng/

Ko kuma ka ziyarcesu a babban shafinsu don karin bayani.⤵⤵
https://startupnigeria.ng/

DUBA WANNAN KUMA.

Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki

Yadda zaku maida lambar wayar ku zuwa ta kasashen waje. in 5min

Yadda Zaku Bude Facebook Account Ba Tare Da Suna Ba.

Yanda Zaka Samu Rancen Kudi Har N100,000 A Layin Etisalat New(9mobile)  

Yadda Ake Connecting Na Android Xender Da Computer. : Android Tutorial 2020. 

Ko kuma Ku ziyarci Page namu mai tâken YADDA AKE....🔗🔗No comments:
Write Comments