Thursday

Home Bidiyo : Wata Sabuwa: Azumin Sitta 6 Shawwal Bidi'a Ne Inji Dr Ahmad Gumi
Dr, Ahmad Gumi Yakaranto A cikin Karatun littafin Imam Malik Cewa Azumin Shida Bayan Ramadan Bidi'a ce.

Asali ma Hadisin Da Ake Kafa Hujja Dashi Ba Ingantacce Bane, cewar ml gumi.Shahararren Malamin addinin Islama dake garin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana cewa azumin guda shida da Musulmai ke yi bayan kammala azumin watan Ramadana, a cikin watan Shawwal bai inganta ba, kuma bidi’a ne.

Gumi ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo daya watsa a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, inda yace a fahimtar babban Malamin addinin Musulunci, Imamu Malik, Azumin Sittu Shawwal bai inganta ba, sahabbai, tabi’ai, duk basu yi ba.

Ga Bidiyon Nan Kasa
A cigaba da jawabinsa, Sheikh Gumi ya bayyana cewa, uwar muminai, matar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Aisha, bata rama azumin watan Ramadan sai a watan sha’aban ma, ma’ana da azumin shawwal ya inganta da an ruwaito tayi.

Bugu da kari Gumi ya bayyana ma masu fahimtar sahihancin hadisin dake kira ga azumin sitta shawwal cewa Malik ya san hadisin, kuma Malik a garin Madina ya rayu kafin Annabi ya cika shekaru 150 da mutuwa, don haka ya san hadisin, amma hadisin bai inganta ba. Daga karshe Malamin ya bayyana cewa akwai raini ga Imamu Malik cikin kiran mutane su yi azumin sitta Shawwal, saboda dama a ko ina akwai masu da’a da bin nagaba da kuma masu yin bore ga nagaba. 
No comments:
Write Comments