Friday

Home Da duminsa: Ala tilas, Ahmad Lawan ya sallami makiyin Buharin da ya ba mukami
A ranar Alhamis shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya sallami sabon hadimin da ya nada, Festus Adebayo, bayan koke-koken masoyan shugaba Buhari da yan jam'iyyar APC kan ta wani dalili zai nada sanannen makiyin Buhari.

Nadin Festus Adebayo, ya tayar da hankalin masoya Buhari musamman a kafar ra'ayin da sada zumunta ta Tuwita inda aka kunnawa sanata Ahmad Lawan wuta kan nadin dan jaridan da ya dade yana yiwa jam'iyyar APC adawa.

A jawabin da mai magana da yawun Ahmad Lawan ya saki, Mohammed Isa, ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawan ya janye nadin da ya yiwa Festus Adedayo kuma fatan alkhairi.

KU KARANTA: Nadin mukamai: Aisha ta kara kwaba wa Buhari magana a fakaice.

Jawabin yace: "Ofishin shugaban majalisar dattawa ta janye nadin da ya yiwa Mista Festus Adedayo matsayin hadimin shugaban majalisa kan yada labarai kuma an sallameshi, yana yi Mista Adebayo fatan alheri a rayuwarsa."

Mun kawo muku rahoton cewa kungiyar Matasa masu ruwa da tsaki jam'iyyar APC a ranar Alhamis sun gudanar da zanga-zangan nuna rashin jin dadin ta kan nade-naden da Shugaban Majalisar Dattawa yayi.

A yayin da ya ke jawabi ga matasan jam'iyyar da ke zanga-zanga, sakataren yada labarai na kasa, Abuh Andrew ya bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya sake bita kan nade-naden da ya yi domin ya samu karbuwa ga dimbin matasan jam'iyyar.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments